2023: Najeriya Ba Ta Bukatar Shugaba Bayarabe Ko Inyamuri – Atiku

Ɗan takarar kujeran shugaban kasa karkashin babbar Jam’iyyar adawa ta PDP Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa shi ‘yan Arewa ke bukata a matsayin shugaban ƙasa a shekarar 2023 ba ɗan takara Bayarabe Ko Inyamuri ba.

Atiku ya bayyana cewa a matsayinsa na dan Arewa, ya shiga kowane lungu da sako na kasar nan kuma ya fahimci ko ina, saboda haka makullan sirri na cigaban Najeriya na a hannun sa.

Tsohon mataimakin shugaban kasan ya bayyana hakan ne yayinda yake amsa tambyar Kakakin kungiyar dattawan Arewa, Hakeem Baba-Ahmed a jihar Kaduna ranar Asabar.

Kungiyoyin yankin Arewacin Najeriya sun shirya taron tattaunawa da dan takarar a gidan tarihin Arewa House dake jihar Kaduna a wani mataki na tunkarar babban zaɓen shekarar 2023.

Kungiyoyin sun hada da Arewa Consultative Forum, Arewa House, Sir Ahmadu Bello Memorial Foundation, Northern Elders Forum, and Arewa Research and Development Project, da sauransu.

Atiku yace: “Abinda kowane dan Arewa ke bukata shine Dan Arewa kuma wanda ya fahimci kowane sashen kasar nan.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply