2023: Kiristocin Arewa Sun Yi Hannun Riga Da Takarar Tinubu

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaba kungiyar dattawa mabiya addinin kirista na arewa, Oyinehi Ejoga, ya yayi kira ga mabiya addinin kirista da kar su marawa jam’iyyar APC baya saboda yadda suka yii shakulatin bangaro da su.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai a taron kolin Zauren taron ƙungiyar kiristocin Arewa da ya gudana a birnin tarayya Abuja.

EJoga yace Wasu marasa kishin yan siyasa zasu yi amfani da duk wata hanya dan su ci zabe, ba tare da la’akarin shin hanyar zata cutar da wasu ba. Yace kun ruguza kanku ta hanyar kin yin abinda ya kamata na bin yadda ake kowanne dan takara shugaba da mataimaki daga addini mabanbanta. amma kun karya tsarin siyasa, wanda san zuciyarku ne ya janyo, kuma muna mai tabbatar muku baku isa ku rusa addinin kiristanci ba.

Mai gabatar da jawabin taro a wajen, Prof. Josaiah Onaolapo, yace zaben shekarar 2023 zai iya zama barazana ga yan Nigeria da kuma tarnaku ga siyasar Nigeria muddin ba’a yi wa kiristocin arewa dai-dai ba.

Yayin da yake jawabi kan makasudin taro mai take; siyasar yau: mafita ga kiristocin arewa, yace Dole ne mabiya addinin kirista su shiga siyasa, domin bayan Allah sai siyasa kan tafiyar da kasa, idan dai mabiya adinin kirista zasu maida hanakli to da tuni bama cikin halin da muke ciki a yanzu. ya kamata ace mun farka daga baccin da muke Onaolapo wanda ya bayyana cewa mabiya addinin na cikin tashin tsanani a yankin in anyi la’akari da yadda a cikin jihohi 19, uku ne kadaii suke mulki a cikinsu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply