2023: Ka Fito Da ‘Ya’yanka Su Taya Yaƙin Neman Zaɓe – APC Ga Kwankwaso

Jam’iyyar APC a jihar Kano ta mayarwa tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, martani kan jawabin da ya yi kan zaben 2023.

Shugaban jam’iyyar na jihar na rikon kwarya, Abdullahi Abbas, ya yi kira ga Kwankwaso cewa ya fito da yaransa na cikinsa lokacin da zai fara yakin neman zabe a 2023.

Abbas ya bayyana hakan ne yayin rantsar da kwamitocin gudanarwa na jam’iyyar a kananan hukumomin jihar 44.

Martanin ya biyo bayan jawabin da Kwankwaso yayi cewa 2023 sai dai a mutu amma ba zasu yarda da ‘inconclusive’ ba.

Idan za a iya tunawa, Kwankwaso ya ce jam’iyyar PDP ba zata sake yarda a maimaita mata abinda ya faru a zaben gwamna na 2019 ba inda aka ce zaben bai kammala ba ‘inconclusive’ a yayin da dan takararta ke kan gaba da kuri’u 26,655.

Labarai Makamanta

Leave a Reply