2023: Jonathan Nada Damar Tsayawa Takara – PDP

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa Prince Uche Secondus ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan na da damar tsayawa takara a babban zaben shekara ta 2023 da ke tafe.

Secondus wanda ya tattauna da ‘yan jarida a ranar Alhamis kan cikarsa shekara uku a matsayin shugaban jam’iyyar, ya ce har yanzu PDP ba ta cimma matsaya kan yin amfani da tsarin karba-karba ba.

Ya yi bayanin cewa jam’iyyar na jiran rahoton kwamitin bitar dalilin faduwar jam’iyyar a zaben shekarar 2019, wanda gwamnan Bauchi Bala Muhammad ke jagoranta, kafin ta yanke wani hukunci na bin tsarin karba karbar.

A baya-bayan nan ne dai gwamnonin jam’iyyar APC suka ziyarci Jonathan a gidansa da ke Abuja don taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa, saidai masu sharhin siyasa na ganin ziyarar akwai siyasa cikinta.

Zaku iya zaban Jonathan idan ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2023 ?

Labarai Makamanta

Leave a Reply