Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar Zabe ta ?asa INEC ta sanar da soke rajistar masu kada kuri’u sama da miliyan guda daga cikin na mutane sama da miliyan 2 da rabi da suka yi rajistar tsakanin 28 ga watan Yunin bara zuwa 14 ga watan Janairun wannan shekara saboda rashin ingancinsu.
Kwamishinan Hulda da Jama’a da kuma ilmantar da mutane kan shirin zaben Najeriya Festus Okoye ne ya sanar da daukar wannan mataki, sakamakon abin da ya kira samun mutanen da suka yi rajistar sama da guda, wanda ya sabawa dokokin zaben kasar.
Okoye ya ce za su ci gaba da gudanar da irin wannan aikin akan mutanen da suka yi rajistar daga watan Fabarairu zuwa Yulin wannan shekara, domin tantance rajistar da kuma tsaftace ta baki daya.
Kwamishinan ya ce, daga karshen watan Oktoba mai zuwa za su fara bai wa ‘yan Najeriya katin zaben na din-din-din kamar yadda suka yi alkawari.
Okoye ya ce da zaran sun kammala aikin tsaftace rajistar, za su sanar da ‘yan Najeriya halin da ake ciki da kuma yawan yan Najeriyar da sunayen su ke cikin rajistar.
A watan Fabarairu mai zuwa ake sa ran gudanar da zaben shugaban kasa da kuma gwamnonin kasar kamar yadda jadawalin zabe ya nuna.