Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gabanin babban zaben shekarar 2023, Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta gargadi yan takara da yan siyasa su daina kamfen a wuraren ibada da hukumomin gwamnati.
Kazalika, an kayyade Naira miliyan 50 a matsayin kudi mafi yawa da daidaikun mutane ko kungiya za su iya bawa dan takara.
Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da INEC ta fitar a Abuja ta hannun kwamishinanta kuma direkta na kwamitin labarai da wayar da kan masu zabe, Festus Okoye. Bisa wannan ka’idojin, hukumar za ta rika saka ido sosai kan yan takarar shugaban kasa kamar Atiku Abubakar, Bola Tinubu da Peter Obi da sauran su.
Okoye ya bayyana cewa ana tattauna game da sabbin ka’idojin ya ce hukumar ta amince da sabbin ka’idojin, wacce ke dauke da sanarwa kan yin ralli, taruka da kamfen. Okoye ya ce an dora dukkan sabbin dokokin zaben a shafin yanar gizo na hukumar, kuma za a bawa jam’iyyun siyasa, kungiyoyin cigaban al’ummma, yan jarida da sauran masu ruwa da tsaki kwafinsu.
Okoye ya bayyana cewa hukumar za ta yi aiki bisa tanadin sabon dokar zabe ta 2022 (da aka yi wa kwaskwarima) dangane da bawa jam’iyyun siyasa tallafi.