Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar za?e ta ?asa INEC ta fara kafe rajistar sunayen masu ka?a ?uri’a a fa?in ?asar yayin da babban za?en 2023 ke ?ara ?aratowa.
Hukumar za?e ta INEC karkashin shugabancin Shugaban hukumar Farfesa Mahmud Yakubu ta ce ta ?auki matakin ne kamar yadda sashe na 9(6) da 199(1) na Dokar Za?e ta 2022 suka tanada don ‘yan ?asa su duba.
Za a ci gaba da kafe sunayen daga 12 zuwa 18 ga watan Nuwamba.
Zuwa yanzu an kafe rajistar a jihohin Sokoto da Oyo da Delta daga cikin jihohin ?asar 36 – har da birnin Abuja.
Al?aluman farko-farko sun nuna cewa mutum miliyan 90.3 ne suka yi rajistar za?en a Najeriya.