2023: INEC Ta Fara Kafe Rijistar Sunayen Masu Kada Kuri’a

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta fara kafe rajistar sunayen masu kaɗa ƙuri’a a faɗin ƙasar yayin da babban zaɓen 2023 ke ƙara ƙaratowa.

Hukumar zaɓe ta INEC karkashin shugabancin Shugaban hukumar Farfesa Mahmud Yakubu ta ce ta ɗauki matakin ne kamar yadda sashe na 9(6) da 199(1) na Dokar Zaɓe ta 2022 suka tanada don ‘yan ƙasa su duba.

Za a ci gaba da kafe sunayen daga 12 zuwa 18 ga watan Nuwamba.

Zuwa yanzu an kafe rajistar a jihohin Sokoto da Oyo da Delta daga cikin jihohin ƙasar 36 – har da birnin Abuja.

Alƙaluman farko-farko sun nuna cewa mutum miliyan 90.3 ne suka yi rajistar zaɓen a Najeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply