2023: Gwamna Inuwa Ya Roki Gwambawa Da Yin Sak

Labarin dake shigo mana daga jihar Gombe na bayyana cewar Gwamnan jihar Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya, ya roki jama’ar jihar su garzaya su karɓi Katin zabensu domin samun damar kaɗa wa APC kuri’unsu a 2023.

Gwamnan yace ɗumbin ayyukan da ya zuba a mulkinsa na farko babban alama ce dake nuna dacewarsa musamman yadda ya maida hankali wajen yaye matsin da mutane ke ciki.

Inuwa Yahaya ya yi wannan jawabin ne yayin kamfe a gundumomi 5 da suka haɗa ƙaramar hukumar Balanga ta arewa ranar Litinin.

Da farko, gwamnan ya ziyarci fadar Bala Waja, babban Basarake a ƙaramar hukumar, Muhammad Danjuma, domin sanar da shi sun zo kamfe a yankin Masarautarsa.

Ɗanjuma ya shaida wa gwamnan cewa ya kwantar da hankalinsa, zai samu kuri’u tuli sakamakon romon ayyukan da ya zuba wa al’umma kamar, “Gina hanyoyi, ɗaukar ma’aikata.” A cewar Basaraken, “Yayin ɗaukar malaman makaranta na kwanan nan, Balanga ce ta zo na biyu cikin jerin waɗanda suka fi amfana.”

Da yake nasa jawabin, kodinetan kwamitin yakin neman zaɓen APC a Gombe, Jamil Gwamna, yace PDP zata sha kaye saboda ba abinda ta tsinana wa al’umma a baya. Gwamna ya yi kira ga masu katin zaɓen su jefa wa APC kuri’unsu tun daga sama har ƙasa domin baiwa gwamnati damar ci gaba da ayyukan da ta ɗauko a zangon farko.

Labarai Makamanta

Leave a Reply