Kungiyar APC Political Alliance (APA), ta yi gargadin cewa rigingimun siyasa a jam’iyyar APC reshen jihar Kaduna wanda suke zargin gwamna Nasir Ahmed El-Rufai na nuna son zuciya wurin tafiyar da mulkin adalci a matsayin sa na shugaba ba mulkin kama karya ba wanda hakan zai sa APC ta rasa kujerar mulkin jihar Kaduna ga jam’iyyun adawa a zaben 2023 dake zuwa.
Kungiyar wacce ta kunshi dattawan mashahuran mutane, mata, matasa, da shugabannin masana’antu ‘ya’yan jam’iyyar APC ne kuma masu goyon bayan jam’iyyar APC, ta ce matakin da Gwamna El-Rufai ya dauka na tilasta wa al’ummar jihar Kaduna ‘dan takarar da yakeson daurawa a matsayin magajinsa, zai raba kan jam’iyyar. , kuma hakan zai sa jam’iyyar ta yi asarar mulki a zaben 2023.
Da yake zantawa da manema labarai a Kaduna, kakakin kungiyar, Alhaji Shehu Abdullahi Mustapha, ya ce Gwamna a ‘yan watannin nan yana tursasa shugabannin jam’iyyar APC na jihar su nada dan takara.
Daga cikin wadanda Gwamna El-Rufia ya yi hasashe akwai Sanata kuma daya daga cikin kwamishinonin sa, matakin da kungiyar ta ce ba ta amince da shi a wajen mafi yawan ‘ya’yan jam’iyyar da shugabannin jam’iyyar a fadin jihar da sauran jama’a ba.
Alhaji Shehu ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran shugabannin jam’iyyar APC na kasa da su kira Gwamna El-Rufai domin ya ceto jam’iyyar daga rugujewa a jihar Kaduna.
Idan har anaso jam’iyyar ta samu nasara a zaben 2023, ya zama wajibi shugaban kasa da sauran masu fada aji du tilasta wa Gwamna El-Rufa’i ya bar dan takara mafi farin jini da mafi yawan ‘ya’yan jam’iyyar da wakilai suka zaba ya fito. a matsayin dan takarar gwamna ba son zuciyar sa ba.” Inji Alh Shehu Abdullahi