Tsohon Sarkin Kano kuma Halifan Tijjaniyya a Najeriya Muhammadu Sanusi II ya yi gargadin cewa Najeriya za ta fuskanci mawuyacin hali fiye da wanda take ciki a yanzu daga shekarar babban za?e dake tafe na 2023.
Sanusi ya yi gargadi mai zafi ga masu burin neman shugabancin kasar da su zurfafa tunani da shirya wa manyan matsalolin da ke fuskantar kasar.
Sanusi ya yi gargadin ne a Abeokuta babban birnin jihar Ogun, inda ya halarci bikin cika shekara 80 da haihuwar jagoran addini na kasar Yarabawa (Babanla Adinni of Egbaland) Chief Tayo Sowunmi.
Halifa Sanusi ya ce, ‘’A gaskiya muna rayuwa ne a kan siradi. A 2015, muna cikin mawuyacin hali. A 2023, za mu kasance a cikin mawuyacin halin da ya fi na 2015.’’
“Ina fatan wadanda suke fafutukar zama Shugaban Kasa, sun fahimci cewa matsalolin da za su fuskanta suna da yawa sosai ninkin-ba-ninkin wadanda muka fuskanta a 2015,’’ in ji shi
Ya kara da cewa, ‘’ Dole ne dukkanninmu mu shirya wa matakai masu tsauri, kuma idan aka dauke su dukkaninmu sai mun dandana kudarmu.’’
Ya ce, ‘’maganin abin ba wai shi ne dukkanninmu mu tsunduma a siyasa ba. Wannan kasar na bukatar ‘yan siyasa na-gari.
Tana bukatar malamai na Musulunci da na Kirista wadanda za su iya tashi tsaye su gaya wa ‘yan siyasa cewa su ji tsoron Allah.’’
‘’Kasar na kuma bukatar kwararrun ma’aikata wadanda za su kalubalanci manufofin ‘yan siyasar.
Tana bukatar shugabannin gargajiya wadanda za su fadi abin da ke zuciyar jama’a. Kowa yana da rawar da zai taka, kuma dole ne mu tashi tsaye”