2023: Dole Mulki Ya Koma Kudu – Babachir Lawal

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal ya ce babu wani ‘dan jam’iyyar APC da ya ke da hurumin hana Asiwaju Bola Tinubu takarar shugaban kasa a 2023.

A wata hira da Mista Babachir David Lawal ya yi da jaridar Punch, ya ce an ma tunbuke Adams Oshiomhole daga kujerar shugaban APC ne saboda rade-radin takarar bola Tinubu.

Lawal ya ce wadanda su ka yi kutun-kutun wajen sauke Oshiomhole su na da burin da su ke so su cinma game da ‘dan takarar APC na shugaban kasa a babban zaben 2023. “Wadanda su ke so Adams Oshiohmole ya yi waje su na harin 2023 ne ido-rufe, a yadda na fahimta, a matsayinsa na shugaban jam’iyya, da wuya ya iya kakabawa jam’iyyarsa ‘dan takarar shugaban kasa.”

“Babu wani wanda ya ke cikin hayyacinsa a jam’iyyar APC da zai hana Tinubu damar neman kujerar shugaban kasa. Babu wani a APC da ya ke da ko da damar tare hanyarsa.”

Dan siyasar ya kara da cewa: “Tun da Arewa ta yi shugaban kasa na wa’adi biyu, sai a mika damar ga yankin Kudu su fito da shugaban kasar da za ayi na gaba.” “Asali ma me Arewa ta samu daga mulkin kasar daga tsawon shekarun da ta yi? Tun bayan mutuwar Janar Sani Abacha, aka jefa yankin cikin rashin tsaro da rashin kyawun tattali.”

“A wannan lokaci mun samu mataimakan shugaban kasa ‘Yan Arewa. Mun samu shugabannin kasa mutanen Arewa, amma saboda wasu dalilai, abubuwa ba su canzawa.” Inji Lawal.

Labarai Makamanta

Leave a Reply