2023: Dole Mulki Ya Koma Kudanci – Yari

Tsohon gwamnan Zamfara Yari ya bayyana yankin da mulkin kasar zai koma a 2023

  • Abdulazeez Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara ya ce jam’iyyar APC za ta tabbatar da ganin mulki ya koma kudancin Najeriya a 2023
  • Yari a kuma bayyana kudirinsa na neman kujerar shugabancin jam’iyyar APC idan ta dawo arewa
  • Sai dai bai fadi yankin kudu da ta cancanci shugabancin kasar ba

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdulazeez Yari, ya ce jam’iyyar APC za ta tabbatar da ganin mulki ya koma kudancin Najeriya a 2023.

Yari ya kara da cewa akwai yuwuwar ya nemi kujerar shugaban jam’iyyar gaba daya idan aka kawo ta arewa.

Tsohon gwamnan, ya ce gyare-gyaren da ake yi a jam’iyyar zai dakile ci gaban matsalolin da jam’iyyar ke fuskanta da kuma abinda ta hadu da shi a zaben 2019.

A wata tattaunawa da Yari, ya ce ana sanya ran mulki zai koma kudu bayan kammala mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

“Ganin yadda tsarin shugabancin kasarmu yake, ya kamata ya tafi kudu. Shugabancin jam’iyyar zai iya dawowa arewa wanda zan shirya karba,” yace a wayar tafi da gidansa.

A yayin da aka tambayesa ko yana daga cikin shugabannin da za su goyi bayan komawar mulki kudu a 2023, Yari ya ce: “Tabbas, haka ya kamata a yi.”

Amma kuma ya ki yin tsokaci a kan wani yankin kudu ne ya kamata ya samu tikitin.

A kalamansa: “Bana son yin tsokaci mai zafi ko wanda zai bata wa wasu rai. Shugabannin APC ne za su yanke hukunci.

“A matsayina na shugaba, bana son yi maganar da za ta bata wa wani rai ko wasu shugabannin rai.”

Yari ya ce wadannan sauye-sauyen da ke faruwa a APC a halin yanzu zai sa jam’iyyar ta gujewa aukuwar abinda ta fuskanta a 2019.

Ya kara da cewa: “abinda muka fuskanta a 2019, shirin taron jam’iyyar da zaben fidda gwani mun yi shi cikin watanni bakwai, wanda hakan bai bamu damar karbar korafin da suka taso bayan zaben fidda gwanin ba.

“Idan muka yi a yanzu,muna da shekaru biyu da rabi don shiryawa zaben 2023.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply