Babban Sakataren jam’iyyar Labour na Kasa Alhaji Umar Ibrahim Mai Ra?umi, yace a halin da ake ciki jam’iyyar ta mayar da hankali ne wajen za?o mataimaki da zai rufa wa ?an takarar shugabancin kasa na jam’iyyar Peter Obi baya daga yankin Arewacin kasar.
Mai Ra?umi ya ?ara da cewar babu shakka tattaunawa ta yi nisa tsakanin jam’iyyar da ?angaren tsohon gwamnan Jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso, amma hakan ba ya nuna cewar dole ne jam’iyyar sai ta ?auki Kwankwaso mataimaki ba.
Babban Sakataren ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a garin Kaduna dangane da babban za?e na 2023 da ke tafe.
Umar mai Ra?umi ya cigaba da cewar Najeriya ta jima tana shan matsa a hannun tsofaffi daga manyan jam’iyyun nan biyu PDP da APC, amma a yanzu lokaci ya yi da ‘yan Najeriya ya kamata su canza taku, su za?i wa?anda suka dace domin ceto kasar daga rugujewa.
“Babban abin da ke jefa Najeriya cikin halin koma baya shi ne siyasar ?angaranci, lokaci ya yi da za a yi watsi da wannan ?abi’a a za?i cancanta ba tare da la’akari da yanki ?abila ko addini ba”.