2023: Ba Na Goyon Bayan Mulki Ya Tsaya A Arewa – Shettima

Tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya ce yana goyon bayan Kudancin Nijeriya ta samar da shugaban kasa na gaba bayan mulkin Muhammadu Buhari.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Shettima ya yi wannan bayani ne a ranar Juma’a, 2 ga watan Yuli, a yayin gabatar da wani littafi.

Tsohon gwamnan ya ce bayan mulki ya zauna a arewa na tsawon shekaru takwas, zai zama adalci a juya shi zuwa kudu.

Ya ce: “Na yarda da daidaito da adalci. Bayan da mulkin ya zauna a arewa na tsawon shekaru takwas, akwai bukatar mika shi zuwa kudu.”

Shettima ya soki kira ga ballewa Shettima, wanda ke wakiltar Borno ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, ya bayyana cewa abin da kasar ke bukata shi ne hadin kai a tsakanin bangarorinta daban-daban, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Ya yi fatali da batun neman ballewar da ke faruwa a wasu sassan kasar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply