2023: Atiku Ya Nada Shekarau Da Saraki Masu Bada Shawara

Ɗan takarar shugabancin kasa a babbar jam’iyyar adawar ta PDP, Atiku Abubakar, ya nada sabbin masu ba shi shawara na musamman don karfafa yakin neman zaɓensa a shekarar 2023.

Wadanda aka nada sun hada da tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, tsohon shugaban majalisan dattawa, Dr.Bukola Saraki da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Sanata Pius Anyim a matsayin masu ba shi shawara na musamman.

Sauran su ne tsohon gwamnan jihar Osun, Prince Olagunsoye Oyinlola da kuma sanata Ehigie Uzamere.

Sai kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Prince Uche Secondus.

Nadin nasu zai fara aiki ne nan take.

Atiku Abubakar ya umarci sabbin wadanda aka nada da su yi amfani da gogewar su ta siyasa domin su tabbatar cewa an samu gagarumar nasara a yakin neman zaɓen 2023.

Labarai Makamanta

Leave a Reply