2023: An Yi Mini Wahayin ?an Arewa Ne Shugaban ?asa – Pastor Elijah

Wani Babban Pastor a Najeriya mai suna Pastor Elijah Ayodele ya bayyana cewa an masa wahayin abinda zai faru a kakar shekarar zabe ta 2023, inda aka tabbatar mishi da cewa ?an Arewa ne zai zama Shugaban ?asa.

Yace a zaben 2023, ‘yan kudu su daina wahalar da kansu maganar tsayawa takarar shuyaban kasa, Saboda Dan Arewa ne zai sake zama shugaban kasa.

Yace amma za’a samu rikici wanda ba’a taba samun irinsa ba a Najeriya, yace mafita kawai shine a canjawa Najeriya fasali.

Ya baiwa Tinubu shawarar cewa kada ya wahalar da kansa tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 dan ba zai ci ba, kamar yanda Daily Post ta ruwaito.

Kalaman Pastor Elijah na zuwa ne a daidai lokacin da batun wanda zai gaji Buhari ke karar ?aukar zafi, inda sashin Kudu suka lashi takobin ganin cewar Mulki ya dawo yankin musamman yankin Kudu maso yamma, inda a hannu guda sashin Kudu maso gabas ke han?oron ganin suma sun ?ana a shekarar 2023.

Related posts

Leave a Comment