2023: An Shawarci ‘Yan Sanda Da Zama ‘Yan Ba Ruwanmu

Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci jami’an ‘yan sandan ƙasar da su zama ‘yan ba ruwana tare da da bijiro da shirye-shirye da za su taimakawa waje ganin an samu sahihin sakamako a zabukan 2023 da ke tafe a fadin ƙasar.

Buhari ya bayyana hakan ne a yau Litinin yayin wani bikin ƙarawa juna sani na kwana uku da aka shiryawa manyan jami’an ‘yan sandan ƙasar domin duba matsalolin barazanar tsaro da ake fuskanta wadanda kuma ake ganin za su kawo cikas a zabukan.

Da yake tabbatar musu da cikakkiyar goyon bayansa gabanin zabukan na 2023, Buhari ya nuna jin dadinsa kan irin sauye-sauye da aka samu a karkashinsa wadanda kuma ke kawo ci gaba musaman ta yadda ‘yan sanda ke gudanar da ayyukansu cikin korewa yanda doka ta tanada.

”A don haka therefore, na hori sufeto janar na ‘yan sanda da ya tabbatar da cewa an bai wa kowane dan kasa dama da kuma hakkinsa na zabar wanda yake so kamar yanda tsarin mulki ya tanada, domin kuma ganin cewa sakamakon zabe ya kasance zabin mutane,” in ji Buhari.

Shugaban ya kuma kara nanata zimmar sa na ganin an gudanar da zabuka masu tsafta cike kuma da gaskiya a shekara ta 2023.

Labarai Makamanta

Leave a Reply