Rahotannin da muke samu daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa wata majiya mai ?arfi ta ce tsagin mataimakin shugaban ?asa ya tuntubi Kwankwaso kan dawowa jam’iyyar APC.
Majiyar tace: “Tattaunawa mai ?arfi ta yi nisa tsakanin Kwankwaso da su. Suna bukatar ya koma jam’iyyar APC, amma har yanzun za?i da muka ba su na nan, muna nan kan bakar mu.”
Da aka tambayi, shin Kwankwaso zai amince su yi takara tare da Farfesa Osinbajo, Majiyar ta ?ara da cewa: “Har yanzun ba’a cimma matsaya ba, abin da zan iya gaya muku shi ne ana cigaba da tattaunawa.”
Har ya zuwa wannan lokaci da muke ciki mataimakin shugaban kasa Osinbajo bai bayyana aniyarsa akan ko zai tsaya takarar shugabancin kasa ko a’a ba, sai dai kungiyoyi da dama na kira a gareshi da yin hakan.
A gefe guda jagoran tafiyar Kwankwasiyya Rabi’u Musa Kwankwaso bai furta matsaya akan tsayawa takarar shugabancin kasa ko zama mataimaki ba, sai dai jama’a na ganin tasirin shi a siyasa zai iya taka muhimmiyar rawa.