Wata kungiyar siyasa mai suna BAT 23, ta kaddamar da yakin neman zabe da kuma tattara masoya ga shugaban jam’iyyar APC, Bola Tinubu a zaben shugabancin kasa da ke zuwa na 2023 a Abuja.
An gano cewa Tinubu na kokarin fitowa takarar zaben shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC a kasar nan.Shugaban kungiyar, Umar Inusa, a yayin kaddamar da fara yakin neman zaben a Abuja a ranar sati, ya ce BAT 23 ta hada da dukkan magoya bayan Tinubu daga jihohi 36 na kasar nan tare da birnin tarayya, Abuja.
Inusa ya yi bayanin cewa, an kafa kungiyar ne domin kafa Tinubu kafin zuwan zaben shugabancin kasa na 2023.Ya ce Tinubu gogaggen shugaba ne wanda yake da kwarewar siyasa da zai iya dasawa daga inda shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tsaya a 2023.
“Tinubu shugaba ne wanda ke mayar da ba komai zuwa komai kuma yana gamsar da jama’arsa da abinda yake da shi. “A zamaninsa na gwamnan jihar Legas, albashin ma’aikata, ayyukan cigaba da na taimako duk basu taba yankewa ba.
“Idan yayi hakan a Legas kuma bamu taba jin cewa jihar Legas ta fada karayar tattalin arziki ba a wancan lokacin, idan ya samu dukkan kasar nan yana kula da ita, ya kenan?
“Mu duba wannan bangaren farko. Wannan shine irin mutumin da muke fatan ya shugabancemu kuma muke goyon bayansa domin sauya akalar kasar nan,” yace.
Tinubu daga yankin kudu maso yamma na Najeriya, ya dade da fara tsara yadda zai zama shugaban kasa.Ya goyi bayan wannan gwamnatin tun daga farkonta kuma ana tsammanin za a saka masa ta hanyar zabensa a karkashin jam’iyyar a 2023.
Jam’iyyarsa ta APC tana tunani tare da saka da warwarar yadda za a yi mulkin karba-karba da yankin kudancin kasar nan bayan mulkin shugaba Buhari a karo na biyu, wanda dan arewa ne daga jihar Katsina.