Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

2023: Adalci Shine Mulki Ya Koma Kudu -El Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El Rufa’i ya nemi a miƙa wa yankin kudancin ƙasar mulki a shekarar 2023 bayan wa’adin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.

Mallam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da BBC.

“Idan ka kalli yadda nake, ba na ɗaukar mutum yayi aiki tare da ni domin shiyyar da ya fito. Cancanta na ke dubawa, ina duba wanda idan aka ba shi amanar jama’a zai riƙe ta yadda ya kamata.”

Ya kuma ce, “A siyasar da ake yi a Najeriya, akwai tsarin da ake bi na karba-karba, inda kowa ya amince cewa idan arewa ta yi mulki shekara takwas, kudu za ta yi mulki shekara takwas.”

Ya ce duk da ba a rubuta tsarin karɓa-karɓan a tsarin mulki ba, amma kowane ɗan siyasa a ƙasar ya san da shi.

‘Shi yasa na fito na ce bayan Shugaba Buhari ya yi shekara takwas, ka da wani ɗan arewa ya nemi muƙamin. A bar ƴan kudu suma su sami shekara takwas.”

Da aka tambaye shi ko da gaske yana da ra’ayin tsayawa takarar shugabancin Najeriya, sai ya ce:

“Ana cewa ina son shugaban ƙasa tun ina ministan Abuja, amma ba na so. Wannan shirme ne.”

Ya kuma ci gaba da cewa Allah shi ke bayar da shugabanci, “ko kana so, ko ba ka so yana iya ba ka. Amma ni ban taɓa neman shugabancin Najeriya ba kuma babu wanda zai ce na taɓa nema.”

Batun rufe kasuwannin Kaduna…

Tun da cutar korona ta bayyana a Najeriya, gwamnatoci sun ɗauki matakan killace al’umominsu a gida inda har ta kai sun kulle makarantu da wuraren aiki da kasuwanni.
A jihar Kaduna, duk da gwamnatin jihar kaduna ta sassauta matakan kullen da ta saka wa al’umar jihar, har yanzu ba ta buɗe wuraren ibada da kasuwanni da makarantu ba.
Wannan ne ya sa ƴan kasuwa ke ƙorafe-ƙorafe kan batun, suna cewa matakin gwamnan jihar na iya kassara su.

Amma gwamnan na Kaduna ya kare kansa daga zargin da ake yi cewa ya ƙi tausaya wa ƴan kasuwan.

“Su ƴan kasuwa suna cewa sun fara bara. Mun ji, amma gara kayi bara kana da rai da ka mutu.”
Ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta buɗe kasuwanni da wuraren ibada ne kawai bayan ta sha ƙarfin annobar.

Ya koka da yadda mutane a jihar ba sa kiyaye wa kamar yadda aka buƙace su.
“Idan muka buɗe masallatai da kasuwanni, cunkoson da muke gani ana yi ƙaruwa zai yi ba raguwa ba. Kuma mutum ɗaya da ke da cutar na iya yaɗa ta ga dubban mutane.”

Exit mobile version