GOMBE 2023: Mailantarki Ya Kwashe Baraden Yakin Isyaku Gwamna, Sun Koma NNPP

Ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe a jam’iyyar NNPP, Khamisu Ahmed Mailantarki, ya na ci gaba da karɓar dandazon manya da ƙananan magoya bayan APC mai mulkin jihar da kuma PDP. A ƙarshen makon nan ne Mailantarki ya haska wa wasu manyan mambobin PDP hanya, su ka bi ta gwadaben da su ka koma NNPP. Mambobin dai zaratan magoya bayan fitaccen ɗan siyasar nan ne Jamil Isyaku Gwamna, waɗanda ake kiran ƙungiyar su da suna Sardauna Dawo-Dawo. A ranar Juma’a ce Mailantarki ya karɓi dandazon ‘yan PDP ɗin a bisa tarbar…

Cigaba Da Karantawa

GOMBE 2023: Mailantarki Kwashe Baraden Yakin Isyaku Gwamna, Sun Koma NNPP

Daga Wakilin Mu Ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe a jam’iyyar NNPP, Khamisu Ahmed Mailantarki, ya na ci gaba da karɓar dandazon manya da ƙananan magoya bayan APC mai mulkin jihar da kuma PDP. A ƙarshen makon nan ne Mailantarki ya haska wa wasu manyan mambobin PDP hanya, su ka bi ta gwadaben da su ka koma NNPP. Mambobin dai zaratan magoya bayan fitaccen ɗan siyasar nan ne Jamil Isyaku Gwamna, waɗanda ake kiran ƙungiyar su da suna Sardauna Dawo-Dawo. A ranar Juma’a ce Mailantarki ya karɓi dandazon ‘yan PDP ɗin…

Cigaba Da Karantawa

Ya Zama Dole A Daina Kai Wa Ofisoshinmu Hari – INEC

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta Farfesa Mahmoud Yakubu ya yi kira ga jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a kasar, da su yi duk abin da za su yi domin ganin an daina kai wa kayayyakin zaben 2023 hari a ko ina. Ya yi wannan kira ne lokacin da yake tattaunawa da majalisar wakilai da kuma kwamiin da yake bincike kan hare-haren da ake kaiwa kan kayayyakin hukumar. Ya ce hukumar ta fuskanci hare-hare 50 cikin jihohi 15 a 2019, Farfesa Yakubu ya bayyana wasu daga cikin…

Cigaba Da Karantawa

Wasanni: Croatia Ta Doke Morocco A Yunkurin Samun Matsayi Na Uku

Rahotannin dake shigo mana daga ƙasar Kasar Qatar na bayyana cewar Croatia ta taka rawar gani a gasar cin kofin duniya da ake fafatawa a Qatar inda ta hau matakin na uku bayan ta doke Maroko da ci biyu da daya. Wannan ne karo na uku da Croatia ke samu kyauta a gasar cin kofin duniya saboda a shekarar 1998 ita ce ta yi ta uku, sai kuma a 2018 ta zama ta biyu a gasar bayan Faransa ta doke taa wasan karshe. A yau Lahadi ne za a buga…

Cigaba Da Karantawa

Iran Ta Damke Shahararriya Jarumar Fina-Finan Kasar

An kama tauraruwar fim Taraneh Alidoosti a Iran yayin da zanga-zangar ƙin jinin gwamnatin ƙasar da ake yi ta shiga wata na huɗu. Kamfanin dillancin labarai na kasar ya ce an kama jarumar ne bayan ta wallafa wani sako da hukumomi suka kira na ƙarya da kuma ƙokarin tunzira masu zanga-zanga a shafinta na sada zumunta. Shahararriyar da ta samu lambobin yabo da dama ta yi Allah-wadai da hukuncin kisan da aka yanke wa wani mai zanga-zanga a farkon watan nan. A makonnin baya, ‘yar fim ɗin ta sanya wani…

Cigaba Da Karantawa

Najeriya Ce Kasar Da Tafi Cancantar A Zuba Hannun Jari A Cikinta – Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce Najeriya ce ta fi dacewa da ƙasar da masu zuba hannun jari daga Amurka za su zuba kudadensu. Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a Washington DC yayin da yake wata tattaunawa ta musamman ta kasuwanci tsakanin Amurka da Najeriya da kuma zauren masu zuba hannun jari, a wani taro da kungiyar hadinkan Amurka da Afrika ta shirya tare da hadin gwiwar ma’aikatar kasuwanci da zuba jari, a gefen taron shugabannin Afrika da Amurka. Yace baya ga yawan da kasar ke da…

Cigaba Da Karantawa