Tinubu Ya Sake Tuntuben Harshe A Wajen Gangamin Taro

Labarin dake shigo mana daga birnin Ikko na jihar Legas na bayyana cewar Dan takara a zaben neman kujerar shugaban kasar Najeriya karkashin jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya sake baranbarama a wajen kamfe. Yayin jawabi da gangamin mabiya dake wajen taro a filin kwallon Teslim Balogun, tsohon gwamnan na Legas yace su je su karbi katin “APV”. Yayinda yake kokarin gyarawa kuma ya sake tafka wata baranbaramar yace APC. Yace: “Shin kuna so na? Ku je ku karbi APV…APC kuma wajibi ne kuyi zabe.” Ba yau farau ba Dan…

Cigaba Da Karantawa

Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da Darasin Tarihi A Makarantu

Gwamnatin tarayya ta sanar da dawo da darasin tarihi a matsayin darasi mai zaman kansa a cikin manhajar ilimi na matakin farko a Nijeriya, shekaru 13 bayan an soke shi. Ministan Ilimi, Adamu Adamu ne ya bayyana hakan a yau Alhamis a Abuja, wajen bikin kaddamar da shirin sake koyar da ilimin tarihi da horar da malaman tarihi a matakin farko. Ya nuna damuwar sa da yadda hadin kai a Nijeriya ya yi ƙaranci, inda mutane su ka saka kabilanci a zuƙatansu, inda ya ƙara da cewa rashin samun ilimin…

Cigaba Da Karantawa

Miliyoyin Yara Na Fuskantar Yunwa A Kasar Habasha – UNICEF

Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce mummunan fari da ba taɓa gani ba cikin gomma shekaru ya jefa miliyoyon yara cikin matsalar rashin abinci da ruwan sha a ƙasar Habasha wato Ethiopia. A wani saƙo da UNICEF ɗin ya wallafa a shafinsa Tuwita ya ce da yawa daga cikin yaran na cikin hatsarin mutuwa sakamakon cutar cutar Tamowa. Yankin gabashin Afirka na fama da mummnan farin da ba a taɓa gani ba cikin gwamman shekaru, bayan da aka kwashe damina biyar ba tare da samun…

Cigaba Da Karantawa

Faransa Ta Kai Zagaye Na Biyu A Gasar Cin Kofin Duniya

Tawagar ƙwallon ƙafa ta Faransa mai riƙe da Kofin Duniya ta zama ta farko da ta samu nasarar zuwa zagaye na gaba a gasar bayan ta lallasa Denmark 2-1. Tun a ranar Juma’a Qatar mai masaukin baƙi ta zama ƙasa ta farko da aka yi waje da ita daga gasar. Kylian Mbappe ne ya ci wa Faransa ƙwallayen, inda mai tsaron bayan Denmark Andreas Christensen ya ci wa ƙasarsa ɗaya. Kazalika, a ɗazu an yi gumurzu tsakanin Saudiyya da Poland inda Poland ɗin ta doke Saudiyya 2-0. Haka kuma an…

Cigaba Da Karantawa

2023: INEC Ta Haramta Yakin Neman Zabe A Masallatai Da Coci-Coci

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a yayin da babban zaɓe na 2023 ke ƙaratowa a Najeriya, hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta hana ‘yan siyasa yaƙin neman zaɓe a masallatai da coci-coci. Hanin na cikin kundin ƙa’idojin kamfe da hukumar INEC ta fitar a ranar Alhamis game da yadda jam’iyyu da ‘yan siyasa za su gudanar da yaƙin neman zaɓuka da kuma adadin kuɗin da za su iya kashewa. “Kar a yi yaƙin neman zaɓe a wuraren ibada, da ofisoshin ‘yan…

Cigaba Da Karantawa