Abin takaici ne halin da nijeriya ta ke ciki na damulewa daga gazawar yaki da cin hanci da rashawa, lalacewar tsaro, rashin tsarin tattalin arziki da ciyar da Nijeriya gaba, uwa uba rushewar ilimin irin na jami’a, wanda shine ke bada tsarin da kowace kasa ta kan hau wajen cigaban ta. Ko ba komai, yau ta nuna wa kowa yadda ginin wannan kasa ke narkewa kadan-kadan, amma jagororin wannan kasar hankalin su yafi karkata wajen siyasar su, ta yadda kawai zasu dawwama a kan karagar mulki da tara dukiya ta…
Cigaba Da KarantawaDay: April 21, 2022
DAMULEWAR NIJERIYA: SHIN ‘YAN NIJERIYA ZASU IYA GYARA KASAR SU?
Ina Kan Ra’ayina Na Sukar Masu Tura ‘Ya’ya Almajiranci – Nafisa Abdullahi
A rubutu da tayi a shafinta na Twitter mai suna @NafisatOfficial, ta ce: “Ya bayyana cewa wasu mutanen ba su ji dadin maganar da nayi ba, na cewa a daina haihuwar ‘ya’yan da ba za a iya daukar nauyinsu ba. Eh, na san an ce ku yi aure ku hayayyafa, amma a ina aka ce ku haifa ‘ya’yan ku watsar da su?. “Kun cika son bada kariya ga abunda kuka san cewa ba daidai bane. Suna cewa wai in bari in yi aure kafin in tsoma bakina a cikin irin…
Cigaba Da KarantawaHarin Jirgin Abuja: Gwamnatin Kaduna Ta Bada Diyyar Miliyan 18
Rahoton dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar Sakataren Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar KADSEMA, Muhammed Mukaddas ya bayyana yadda gwamnatin Jihar Kaduna ta amince da bayar da Naira Miliyan 18 ga mutane 9 wadanda mummunan harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya ritsa da su. Mukaddas ya bayyana hakan ne a ranar Laraba inda ya ce a ranar 19 ga watan Afirilu gwamnatin ta amince da bayar da Naira Miliyan 2 ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu ta dalilin harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna. Mukaddas…
Cigaba Da Karantawa2023: Inyamuri Ya Kamata Ya Zama Shugaban Kasa – Afinifere
Shugaban majalisar tuntuɓa ta ƙabilar Yarabawa, Afenifere, Cif Ayo Adebanjo ya nemi masu neman takarar shugabancin Najeriya daga yankin kudu maso yamma da su haƙura. Shugaban ƙungiyar al’ummar Yarabawa ya ce ya kamata ‘yan takarar yankin nasu kamar Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo su bar wa ‘yan ƙabilar Igbo don samar da shugaban ƙasa na gaba a 2023. Jagoran ya bayyana hakan ne cikin wata hira da jaridar Punch ranar Talata, yana mai cewa “rashin adalci ne ɗan kudu maso yamma ya zama shugaban ƙasa bayan…
Cigaba Da KarantawaBa Zan Bari A Sake Karya Doka A Najeriya Ba – Buhari
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su guji mutanen da ke hankoron ganin sun karya doka a kasar. Wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Malam Garba Shehu ya aike wa manema labarai ta ambato Shugaba Buhari yana mai tabbatar wa ‘yan kasar cewa ba zai kyale wani ya karya dokokin kasar ba. ”Muna da kasa, muna da albarkatun kasa da kuma mutane. Sai dai ban san dalilin da ya sa wasu ke da niyyar ba…
Cigaba Da KarantawaFarashin Fom Din Takarar APC Ya Razana ‘Yan Najeriya
Ƴan Najeriya na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu kan tsadar fom na takara a jam’iyyar APC inda ta ke sayar da fom ɗin takarar shugaban ƙasa a naira miliyan 100. A ranar Laraba ne majalisar zartarwar jam`iyyar ta tabbatar da jadawalin zabukan fitar da gwani na masu neman mukamai daban daban da kuma farashin fom na takara. Majalisar zartarwar jamiyyar ta yi zaman ne ƙarƙashin jagorancin shugaba Buhari da shugabannin jamiyyar na kasa da jihohi da gwamnoni da sauran jiga-jiganta daga sassan Najeriya inda aka amince da farashin fom na…
Cigaba Da Karantawa