Gwamnatin Nijeriya Za Ta Haramta Shigo Da Madara Daga Shekarar 2022, domin inganta kayayyakin haɗin cikin gida yadda Najeriya zata tsayu da ƙafafuwan ta, ta wannan ɓangare.
Ministan noma da raya karkara, Sabo Nanono ya yi bayanin cewa ma’aikatarsa na shirye-shirye domin tabbatar da samar da kayayyaki don samar da madara a dukkanin fadin kasar.
Da wannan dalilin ne gwamnatin tarayya za ta haramta shigo da madara cikin kasar daga shekarar 2022.
Nanono ya bayyana hakan ne a yayinda yake zantawa da manema labarai a Abuja, a wani taro kan ranar abinci ta duniya na shekarar 2020.