Za A Fara Rabawa ‘Yan Najeriya Dubu Biyar -Biyar Kowane Wata

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za a baiwa ‘yan Nijeriya milyan 24, kowannensu naira dubu 5000 na tsawon watanni shida daga cikin kokarin gwamnati mai ci na fitar da mutane daga kangin talauci. Ma’aikatar harkokin agaji da magance annoba ce ta bayyana hakan a ranar Talata, 19 ga watan Janairu. Da take Karin haske a kan lamarin a Abuja ta wani jawabi daga hadimarta Nneka Anibeze, ministar walwala, Hajiya Sadiya Farouq, ta ce shirin zai gano tare da yi wa mutanen da ba a yiwa rijista a baya ba…

Cigaba Da Karantawa

Kul! Da Korar Fulani Daga Jihar Ondo – Buhari Ga Gwamna

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta soki umarnin gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, na korar makiya daga dazukan Jihar Ondo. Idan baku manta ba, gwamnan ya bawa kwana Bakwai da su bar dazukan jihar nan, daga ranar Litinin 18 ga Janairun 2021,” a cewar gwamnan. A martanin ta ranar Talata, fadar shugaban kasa ta bakin mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya ce Mr Akeredolu, babban lauya, “ba za a tsammaci ya kori dubban makiyan da rayuwar su ta dogara da jihar ba bisa yan ta’addan da suka mamaye daji…

Cigaba Da Karantawa

Sai Mun Cire Hassada Da Girman Kai Kafin Samun Zaman Lafiya A Arewa – Dingyaɗi

Ba Shakka Muddin Muna Son Ganin Ci gaba Da Zaman Lafiya A Arewarmu Sai Mun Debe Hassada, Kwadayi Da Girman Kai A Tsakanin Juna. Cin Duga-dugan Juna Da Manyan Arewa Keyi Ba Abin Da Yake Haifarwa Illa Kiyayya Da Ganin Kyashi Da Tozarta Juna Tare Da Rarrabuwar Kawuna. Arewa Ta Shiga Gararin Da Bata Taba Shiga Ciki Ba A Sakamakon Rashin Hadin Kai, Mutunta Juna Da Son Kai Na Wasu Dake Ganin Ala Dole In Ba Abin Da Suke So Ba; Sai Dai Kowa Ya Rasa. Ba Ruwansu Da Neman…

Cigaba Da Karantawa

Gobarar Kasuwar Sokoto: Gwamnan Kebbi Ya Bada Gudummuwar Miliyoyi

Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya kai ziyarar jaje ga Gwamnatin jihar Sokoto sanadiyar gobarar da ta kone sabuwar Kasuwar garin Sokoto, inda ya samu tarbo daga takwararsa Gwamnan Jihar Sokoto Rd. Hon. Aminu Waziri Tambuwal. Haka zalika Gwamna Bagudu ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Kebbi ta bada gudummuwar maira milyan talatin ( 30,000000). A nasa bangaren, Gwamna Tambuwal ya yi godiya ga Gwamna Bagudu bisa wannan gudummuwa da Jihar Kebbi ta baiwa ‘yan kasuwar Jihar Sokoto da Iftila’in gobara da ya shafi Yan Kasuwar Jihar Sokoto inda…

Cigaba Da Karantawa

Sai Mun Haɗa Kai A Afirka Kafin Mu Magance Matsalar Tsaro – Buhari

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sake jaddada bukatar kasashen Afirka makwabta su kasance masu haɗin kai da kiyaye muradun juna a koda yaushe, domin hakan kaɗai shine hanyar da za ta taimaka wajen magance matsalar tsaro da ke addabar yankin. Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin shugaban kasar Benin, Patrice Talon, wanda ya kai ziyarar gani da ido a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Talata. Buhari a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da yada…

Cigaba Da Karantawa