Sukar Musulunci: An Buƙaci Kukah Ya Gaggauta Barin Sokoto

Kungiyar Musulim Solidarity Forum dake jihar Sokoto ta bayyanawa Bishop Kuka cewa ko dai ya daina sukar Musulmai da fadar maganganu mara dadai sannan kuma ya bada hakuri ko kuma ya bar Sokoto. Shugaban kungiyar, Farfesa Isa Maishanu ya bayyana a sanarwar da suka fitar cewa Bishop Kuka na son kawowa zaman lafiya dake tsakanin Musulmai da kiristocin Sokoto tangarda. Kungiyar ta kuma gayawa shuwagabannin musulmai cewa su daina nunawa Kuka Kara saboda yana amfani da wannan yana yiwa Musulunci katsalandan. Kungiyar tace a watan Fabrairu na shekarar 2020 Kuka…

Cigaba Da Karantawa

Kiristoci Sun Yaba Ƙoƙarin Da Nake Yi Wa Musulunci – Kabara

Shahararren mutum a jihar Kano wanda ake kira Abduljabbar Kabara ya bayyana cewa kiristoci sun fara yaba masa saboda kokarinsa wajen tsaftace addinin musulunci. Abduljabbar Kabara wanda ke shan suka da caccaka daga bangarorin Malaman musulunci ya jaddada cewa aikin alkhairi yake yi wa addini wanda hakan zai amfanar da musulunci. “Akwai kiristan da yayi waya da daya cikin masu daukan karatunmu, wani Faada, daga baya aka saka min hirar na saurara, wannan kirista ya bayyana cewa yana bibiyar karatukana, wannan kirista dan kwangila ne da ake daukar su su…

Cigaba Da Karantawa

Kiristoci Sun Yaba Ƙoƙarin Da Na Ke Yi Wa Musulunci – Kabara

Shahararren mutum a jihar Kano wanda ake kira Abduljabbar Kabara ya bayyana cewa kiristoci sun fara yaba masa saboda kokarinsa wajen tsaftace addinin musulunci. Abduljabbar Kabara wanda ke shan suka da caccaka daga bangarorin Malaman musulunci ya jaddada cewa aikin alkhairi yake yi wa addini wanda hakan zai amfanar da musulunci. “Akwai kiristan da yayi waya da daya cikin masu daukan karatunmu, wani Faada, daga baya aka saka min hirar na saurara, wannan kirista ya bayyana cewa yana bibiyar karatukana, wannan kirista dan kwangila ne da ake daukar su su…

Cigaba Da Karantawa

Duk Ranar Da Buhari Ya Bar Mulki Sai Talakawa Sun Yi Kuka – Shugaban Manoma

Alhaji Shuaibu Wakili, Shugaban kungiyar masu noman shinkafa na jihar Katsina, ya bayyana cewa tun da ake mulki a Nijeriya, ba’a taba samun Shugaban Kasa da ya kula da rayuwar talakka ba, kamar ta shugaban kasa Muhammadu Buhari a irin kokarin tallafawa Kungiyoyin manoma a kasar nan, idan da ace za’a iya gyaran kundin mulki, Ina goyan bayan ya zarce ya zama Shugaban Kasa na din-din, saboda duk ranar da ya bar mulki, wallahi talakkawan sai sun yi kuka da idanun su a kasar nan. Alhaji Shuaibu Wakili, ya bayyana…

Cigaba Da Karantawa

Muna Dab Da Kawo Ƙarshen ‘Yan Bindiga – Gwamnatin Katsina

A kokarinta na kawo karshen matsalar tsaro da wasu kananan hukumomin jihar Katsina, ke fama da ita, Kwararren masanin tsaro Kuma mai baiwa gwamna Aminu Bello Masari shawara kan harkokin tsaro, Alhaji Ibrahim Ahmad Katsina ya ce wannan sabuwar hanya da muka bullo da ita za ta kawo karshen matsalar rashin tsaro da jihar ke ciki. Ibrahim Ahmad Katsina ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke tattaunawa da RARIYA a ci gaba da shirye-shirye wani taron karawa juna sani da ofishin sa zai shiryawa manema labarai a ranar…

Cigaba Da Karantawa

Zaɓen 2023: Za Mu Sauya Tsarin Amfani Da Card Reader – INEC

Hukumar zaben Nijeriya INEC ta ce ta fara bitar tsarin fasahar da take amfani da shi a zabuka da manufar shiga sabbin hanyoyin inganta zaben kasar kafin nan da shekara ta 2023. ”Babban daraktan yada labarai na INEC Nick Dazing ya bayyana haka a ranar Talata, lokacin wani taron karawa juna sani da sashen ya shirya domin bitar littafin wayar da kan masu zaben, wanda ya gudana a Birnin Keffi na jihar Nasarawa. ”Da yake magana da ‘yan jarida kan muhimmancin taron wanda hukumar ta shirya hadin guiwa da Gidauniyar…

Cigaba Da Karantawa

Ƙetare: An Haramta Amfani Da Kafafen Sada Zumunta (Social Media)

Babban Daraktan Hukumar Sadarwar Uganda Irene Sewankambo ya umurci kamfanonin sadarwar kasar su dakatar da duk wata dama ta yin amfani kafafen sadarwa na zamani da hanyoyin tura sakonni ta intanet nan take. Wannan umurni da aka bayar ranar Talata, na zuwa ne kasa da kwana biyu kafin zaben shugaban kasar da za a yi a ranar Alhamis. Wani da ke da kusanci da hukumar sadarwar kasar ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an fara bada umurnin ne a wani kiran waya da aka yi wa kamfanonin sadarwar…

Cigaba Da Karantawa

Garba Shehu Bai San Aikinsa Ba – Dattawan Najeriya

Dattawa masu kishin Nijeriya sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kori mai taimaka masa ta fuskar yada labarai Garba Shehu, saboda zarginsa da suke na rashin tauna magana kafin ya fade ta. Wannan kira ya zo ne bayan wata magana da Shehun ya yi, inda yake ikirarin cewa Shugaban kasa ne kadai ke da ikon kayyade wa’adin shugabannin tsaron kasar. Da yake magana kan kin sauke hafsoshin tsaron da Buhari bai yi ba lokacin da ake fira da shi a wani gidan talabijin, Garba Shehu ya ce babu wani…

Cigaba Da Karantawa

Za Mu Tura Sabbin Kuratan Sojin Da Aka Ɗauka Dajin Sambisa – Buratai

Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya, Tukur Buratai, ya bayyana cewa Hukumar Sojojin Najeriya za ta yi tankade da rairaye da zazzage a daukar kuratan sojoji, ta yadda sai wadanda su ka cancanta kadai za a dauka aiki. Ya ce babu wani gurbi ko guda daya da za a dauki wanda bai cancanta ba a jefa cikin aikin soja. Laftanar Janar Buratai dai ya yi wannan ban-tsoron a lokacin da ya ke jawabi wajen tantanace kuratan sojoji a Dajin Falgore, cikin Jihar Kano a ranar Litinin. Ya ce wannan aikin tantance sabbin…

Cigaba Da Karantawa

Borno: Sama Da Yara 1000 Ne Zulum Ya Mayar Makaranta

Gwamnan jihar Barno Farfesa Babagana Umara Zulum ya sanya yara 1,163 na mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da muhallinsu a wata makaranta a garin da aka kwato daga hannun masu tayar da kayar baya a jihar ta Borno. Gwamnan, wanda ya sanya ido a kan sanya yara ‘yan gudun hijirar a garin Damasak, a ranar karshe ta ziyarar da ya kai yankin ranar Litinin, ya ce atisayen wani yunkuri ne na tabbatar da ci gaba mai dorewa. Ya yi kira ga iyaye da su bar ‘ya’yansu su shiga…

Cigaba Da Karantawa

Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Kaddamar Da Sabbin Hare-Hare

A cigaba da kai hare haren ta’addanci da ‘yan Bindiga ke yi a yankin Arewa maso yammacin Najeriya, a yammacin jiya wasu ‘yan Bindiga da ake kyautata zaton Fulani ɗauke da muggan makamai sun kaddamar da hari a yankin ƙaramar Hukumar Kauru ta jihar Kaduna. Harin ya yi sanadin rasa rayukan wasu mazauna kauyukan Bakin kogi da Narido dake yankin ƙaramar Hukumar, da jikkata wasu adadi masu yawa gami da salwanta na tarin dukiyoyin jama’a. Dakarun sojin rundunar Operation Safe Haven sun sanar da gwamnatin jihar kaduna batun wannan hari…

Cigaba Da Karantawa

Ƙaddara Ce Ta Hanani Zama Shugaban Majalisa A 2015 – Lawan

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan, ya ce bai zama shugaban majalisar dattijai a shekarar 2015 ba saboda ba’a lokacin Allah ya tsara zai hau kujerar ba, domin komai na rayuwa yana tafiya ne bisa ƙaddara da hukuncin Ubangiji. Shugaban Majalisar ya bayyana hakan ne a yayin taron bikin zagayowar ranar haihuwar shi Shekaru 62 da ya gudana a babban birnin tarayya Abuja. Da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai, Lawan ya ce duk da bai samu nasara a wancan lokacin ba, hakan bai hana shi yin aiki hannu…

Cigaba Da Karantawa

Buɗe Masallatai Da Coci-Coci Ne Silar Dawowar CORONA Karo Na Biyu – Gwamnatin Tarayya

Shugaban Kwamitin PTF kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya bayyana cewa gaggawar bude makarantu, Masallatai da Coci-Coci ne suka yi sanadiyyar kara yaduwar Korona a Kasar nan. Mustapha ya fadi haka ne ranar Litini a ganawa da kwamitin ta yi da manema labaraia Abuja. Sannan kuma bude filayen jirage sama domin tashi da saukar jiragen matafiya ya taka mahimmiyar rawan wajen kara yada cutar tun a karshen watan Nuwamba 2020. Sakamakon wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa a kowani mutum shida da za ayi wa gwajin Korona…

Cigaba Da Karantawa