CORONA: An Kulle Jihar Ekiti

Gwamnatin jihar Ekiti ta saka dokar hana fita a fadin jihar Ekiti inda dokar za ta fara aiki daga yau Litinin, 11 ga watan Janairun 2021. Dokar za ta rinƙa aiki ne daga 8:00 na dare zuwa 6:00 na safe. Gwamnatin jihar dai ta saka wannan doka ne a yunƙurinta na daƙile yaɗuwar annobar korona. Hakan ya sa gwamnatin ta kuma hana taruwar mutum sama da 20 a wuri guda har sai abin da hali ya yi. Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Akinbowale Omole ya bayyana cewa gwamnati na son…

Cigaba Da Karantawa

Haƙurinmu Ya Ƙare Maza Muke Buƙata – Matan Gidan Yari

Matan dake a gidan gidajen yarin kasar Kenya sun roki gwamnatin kasar da ta bar samarinsu su dinga saduwa dasu in sun kawo musu ziyara. Wasu daga cikin matan sun koka kan cewa an yanke musu hukuncin daurin rai-da-rai ne kuma suna bukatar a riƙa biya musu bukata. Mai magana da yawun ƴan Matan gidan yarin Sofia Sweleh wadda aka yankewa hukuncin daurin rai-da-rai ce ta shaida hakan a madadin sauran ƴan uwanta da suke tsare a tare. Bincike ya nuna cewar ana samun irin wadannan matsaloli sosai a gidajen…

Cigaba Da Karantawa

Cire Haraji: Motoci Da Kayayyakin Abinci Za Su Faɗin Warwas A Najeriya

Kudirin tattalin arziki na shekarar 2020, ya zo da sababbin manufofi da ake sa ran za su jawowa Najeriya kudin shiga tare da zabubar da tattalin kasar, kamar yadda Jaridar The Cable ta ruwaito. Jadawalin Wasu daga cikin amfanun wannan sabuwar dokar da ake kyautata zaton talakawan kasar Nijeriya zasu sha jarmiya.👇👇👇 Motoci za su rage tsada, an dawo da harajin shigo da motoci 5% daga 35%. Babu haraji a kan duk ma’aikatan da albashinsu bai wuce N30, 000 ba. An daina cire wani kaso da sunan kudin hatimi idan…

Cigaba Da Karantawa

Za A Iya Haɗa Lambobin Waya 7 Da Katin Ɗan Ƙasa Guda – Pantami

Ministan Sadarwa da tattalin arzki na digital Sheikh Dakta Isa Ali Pantami, ya bayyana cewa za a iya hada layukan waya dabam-dabam har bakwai da lambar katin zama dan kasa guda daya. Sheikh Pantami ya fadi haka ne a lokacin da ya amsa tambayoyi a wani shirin gidan talbijin din Channels dake Abuja. ”Mun kirkiro manhaja da za ka iya hada layuka bakwai da lambarka na katin zama dan kasa nan take cikin sauki. Mun yi haka ne domin a samu saukin hada layukan ba tare da an wahala ba.…

Cigaba Da Karantawa

Kannywood: Duk Wanda Ya Saki Mace Cikin Fim Matarshi Ta Gida Ta Saku – Dr Bashir Umar

Ɗaya daga cikin manyan Malam Addinin Musulunci a birnin Kano Shiekh Dakta Bashir Aliyu Umar Alfuqan, ya yi fashin baki game da yin sakin aure a cikin wasan kwaikwayo (fim). Dakta Bashir Alfurqan, ya ce dukkan wani dan wasan fim da ya furtawa matar sa ta ciki shirin fim saki, to babu shakka matar sa ta gida ya saka. Babban Shehin Malamin ya ce babu wasa a sakin aure, indai ka sake ka furta saki a wasan kwaikwayo, to lallai matar ka ta gida ka saki babu shakka a kan…

Cigaba Da Karantawa

Bauchi: Mutane 20 Sun Ƙone A Hatsarin Mota

A yammacin lahadi ne motoci biyo sukayi taho mu game, akan titin Maiduguri dake garin Bauchi inda pasinjoji ashirin suka rigamu gidan gaskiya nan take. Shaidun gani da ido since hatsarin wanda ya aiku daidai yan mangorori akan titin zuwa Maiduguri kusa da gari Tirwun kimanin murabba’i uku da isa babban birnin Jihar (3km) wanda a cewar su nan take motocin suka kama da wuta ko kafin Yan kwana-kwana so iso wajen tuni mutum ashirin 20 suka cika, mutum biyukima aka ciresu da ransu. Hakan wadanda suka ga yadda hatsarin…

Cigaba Da Karantawa

Boko Haram Da ‘Yan Bindiga Za Su Zama Tarihi A Wannan Shekarar – Buhari

Shugaba ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa a cikin shekarar nan ta 2021, za’a kawo karshen kungiyar Boko Haram da sauran ‘yan ta’adda, tare da neman ‘yan kasa su tallafawa rundunar soji da addu’a domin kai wa ga samun nasara. Shugaba Buhari ya bayyana dalilai hudu da zasu ba gwamnati damar kawo karshen kungiyar Boko Haram a wannan shekara ta 2021. Shugaba Buhari ya bayyana cewa ko kadan ba ya jin dadin ta yadda ake asarar rayuka a kasar tare da bayyana cewa nan bada dadewa ba za’a kawo karshen…

Cigaba Da Karantawa