Katsina: Na Ci Duka Kamar Jaki A Hannun ‘Yan Bindiga Bayan Gano Ni Soja Ne

Wani Soja, mai mukamin Saje da ke aiki a Maiduguri, da ya zo ganin gida da kuma jinyar raunin da ya samu a kugun sa, ya bayyana yadda yan bindiga suka sace shi da yadda suka kuntata ma shi a lokacin da ya ke hannun su na tsawon kwanaki ashirin da shidda. Sojan ya ci gaba da cewa daga Maiduguri na taho domin yin jinyar raunin da na samu, sun tsaya a wani daji na wajen Gurbin Baure, na take suka fara barin wuta, har suka fashe mani tayoyi, suka…

Cigaba Da Karantawa

Ta’addanci: Sama Da Mutane Miliyan Biyu Sun Zama ‘Yan Gudun Hijira

Ministar agaji da kare aukuwar ibtila’i ta Nijeriya Sadiya Umar Farouk, ta ce yanzu haka kasar na da yawan mutane sama da miliyan biyu da suka rabu da muhallansu. Ta ce wadanda abun ya shafa sun rasa muhallan nasu ne ta sanadiyyar ayyukan ta’addanci da ‘yan bindiga ko kuma rikicin kabilanci. Ministar ta fadi haka ne a lokacin da take ganawa da ‘yan jaridar fadar shugaban kasa a ranar Alhamis, bayan wata ganawa da ta yi da shugaba Buhari a Abuja. Sadiya, ta ce ta kawo wa shugaba Buhari ziyara…

Cigaba Da Karantawa

Kaduna: Harin ‘Yan Bindiga Ya Hallaka Mutum Huɗu

Wasu ‘yanbindiga sun kai hari a kauyen Katarma da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna inda suka kashe mutum hudu ciki har da ‘yan banga tare da sace wasu mata. Wani rahoton tsaro ya nuna cewa da fari ‘yan bindigar sun yi artabu da ‘yan bangar kauyen kafin daga bisani dakarun tsaro su kawo masu dauki. Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, yana mai cewa jami’an tsaro sun yi nasarar ceto…

Cigaba Da Karantawa

Na Lashe Shekaru Ina Sayar Da Mushen Kaji A Maiduguri – Ebere

Rundunar jami’an tsaron farin kaya Civil Defence a Jihar Borno ta yi nasarar damke wani mutum da ya daɗe yana safarar mushen kaji gami da sayarwa jama’a a Jihar Borno tsawon shekaru. Lokacin da yake amsa tambayoyi a helkwatar rundunar, ya tabbatar da cewar a kalla ya yi nasarar sayar da Mushen Kaji sama dubu bakwai a Jihar Borno da kewaye. Ɗan kimanin shekaru 33 Mutumin mai suna Hassan Ebere, ya ƙara da cewar bai san adadin shekarun da ya shafe yana gudanar da muguwar sana’ar ba a Maiduguri da…

Cigaba Da Karantawa

Katsina: Yadda ‘Yan Bindiga Suka Azabtar Dani Da Jikokina – Tsohon Da Ya Kuɓuta

Dattijo Alhaji Ado, wanda ‘yan bindiga suka sace da jikokinsa guda biyu da ke garin Dodo, a yammacin garin Wagini da ke karamar hukumar Batsari a jihar Katsina, ya bayyana irin ukubar da ‘yan bindigar da suka sace su kwanaki goma sha ukku tare da mutanen garin su, talatin da biyar maza da mata, suka kora mu daji kamar awaki ba takalma a kasa mu ka yi ta tafiya har muka isa maboyar su. Alhaji Ado ya bayyana irin rayuwar da suka yi a tsawon wadannan kwanakin a hannun su,…

Cigaba Da Karantawa

Katsina: Yadda ‘Yan Bindiga Suka Azabtar Dani Da Jikokina – Dattijon Da Ya Kuɓuta

Dattijo Alhaji Ado, wanda ‘yan bindiga suka sace da jikokinsa guda biyu da ke garin Dodo, a yammacin garin Wagini da ke karamar hukumar Batsari a jihar Katsina, ya bayyana irin ukubar da ‘yan bindigar da suka sace su kwanaki goma sha ukku tare da mutanen garin su, talatin da biyar maza da mata, suka kora mu daji kamar awaki ba takalma a kasa mu ka yi ta tafiya har muka isa maboyar su. Alhaji Ado ya bayyana irin rayuwar da suka yi a tsawon wadannan kwanakin a hannun su,…

Cigaba Da Karantawa

Najeriya Ta Sukurkuce A Mulkin Buhari – Kukah

A cikin hudubarsa ta baya-bayan nan ya koka kan yadda Najeriya ta zama kazamar kasa, cike da tarkace, yaudara, karya, cin amana, da kuma rikita-rikita inda duhu ya mamaye komai. Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 6 ga watan Janairu, yayin da yake gabatar da hudubarsa a babban cocin Katolika na St Joseph, Kaduna, a lokacin da ake gudanar da hidimar Archbishop Peter Yariyock Jatau, Archbishop na Kaduna Catholic Diocese. Shugaban addinin wanda ya kare kansa a sakonsa na Kirsimeti na 2020 wanda ya haifar da martani, ya dage…

Cigaba Da Karantawa

CORONA: Za A Yi Wa Buhari Da Osinbajo Allurar Rigakafi A Bainar Jama’a

Babban daraktan hukumar kiwon lafiya a matakin farko (NPHC), Faisal Shu’aibu, ya ce za’a fara yi wa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da mataimakinsa, Yemi Osinbajo, allurar riga-kafin cutar COVID-19 kai tsaye ta akwatin talabijin. Kimanin kwayar maganin riga-kafin cutar ta COVID-19 100,000 ake sa ran shigo da su ƙasar nan a ƙarshen watan Janairu, kamar yadda TheCable ta rawaito. Da ya ke ganawa da kwamiti na musamman kan yaƙi da yaɗuwar cutar korona a Abuja, Shu’aibu ya ce za’a nuna yin riga-kafin kai tsaye ta kafar talebijin a ƙoƙarin wayar…

Cigaba Da Karantawa

Gwamnatin Tarayya Ta Janye Ƙarin Farashin Kudin Lantarki

Ma’aikatar da ke kula da harkokin wutar lantarki ta ƙasa ta dakatar da wani ƙarin kuɗin wuta da aka yi, bayan barazanar da kungiyoyin ƙwadago suka yi na sa-kafar-wando-guda da gwamnati. A wannan makon ne aka sanar da ƙarin farashin, wanda mahukunta suka danganta da hauhawar farashi, inda kilowatt ɗaya ya tashi daga naira biyu ya koma naira huɗu. Ma’aikatar wutar ta hanzarta sanar da janye karin kuɗin wutar da aka yi ne, kamar yadda ta ce domin ta fahinci cewa an jahilci ƙarin, saboda wasu na cewa ya kai…

Cigaba Da Karantawa