Kimanin Biliyan Uku Za A Kashe Wajen Tafiye-Tafiyen Buhari A 2021

Ofishin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai kashe Naira Biliyan 2.42 a kan tafiye-tafiye na cikin gida da kasashen ketare a 2021 yayin da fadar shugaban kasa za ta kashe Naira Miliyan 135.6 a kan lemuka kamar yadda ya ke rubuce a cikin kasafin kudin bana. A ranar 31 ga watan Disamban 2020 ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan kasafin kudin kasar nan na 2021. A kasafin kudin, jimillar kudin da aka warewa ofishin shugaban kasan na manyan ayyuka shine N3.82bn sai N2.76bn na ayyukan yau da…

Cigaba Da Karantawa

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rancen Kuɗaɗen Ajiyar ‘Yan Najeriya Dake Banki

Duk da rashin amincewar masu hannun jari, da sauran masu ruwa da tsaki a harkar kudade, gwamnatin tarayya na shirin aron kudaden ‘yan Najeriyan da ke asusun da aka dade ba’a waiwayesu ba, da kuma kudaden masu hannun jarin da aka dade ba’a bibiya ba. Gwamnatin zata samu daman yin hakan ne bisa dokar kudin Shekarar 2020 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu. Ƙarkashin sashe na 12 na dokar, an bayyana cewa za’a iya aron kudaden masu hannun jarin da ajiyan da mutane wanda suka kai shekaru…

Cigaba Da Karantawa

Tsaro: Mun Fi Samun Tallafi Daga Turai Fiye Da Kasashen Larabawa – Zulum

Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce kasashen Turawa sun fi nuna damuwa da halin da Jihar Borno ke ciki na taɓarɓarewar tsaro da barazanar Ƙungiyar ta’addanci ta Boko Haram fiye da ƙasashen Larabawa. Zulum ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin jakadan Falasdinawa a fadar gwamnatin jihar Borno dake birnin Maiduguri cikin makon nan. A cewar gwamnan, babu wata kasar Larabawa a baya da ta ba Jihar Borno tallafin da kasashen Turai suka bayar Sakamakon ƙalubalen hare-hare na Boko Haram da sauran ayyukan ta’addanci masu…

Cigaba Da Karantawa

Kano: Za A Koma Biyan Karancin Albashi Na Dubu 18

Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Abdullahi Umar Ganduje ta sanar da daina biyan ma’aikatanta karancin albashin N30,000 tare da gaggauta komawa biyan karancin albashin zuwa N18,000 kamar yadda aka saba kuma aka gada. Gwamnatin ta bayyana cewa hakan ya biyo bayan karayar tattalin arzikin da aka shiga saboda Covid-19 Annobar ta yi mummunar illa ga tattalin arzikin jihohi da dama na Najeriya ballantana jihar Kano. A yayin tabbatar da wannan sauyin mai magana da yawun Gwamna Umaru Ganduje, Salihu Tanko-Yakasai, ya ce halin da kasar nan ta shiga…

Cigaba Da Karantawa

Ba Mu Shirya Komawa Karatu Yanzu Ba – Ɗaliban Jami’ar Bayero

Alamu na nuna cewa da yawa daga cikin ɗaliban jami’ar Bayero dake Birnin Kano BUK ba za su koma karatu a ranar 18 ga Janairu ba kamar yadda hukumar gudanarwar jami’ar ta bayar da sanarwa ba. Kwana ɗaya da sanarwar janye yajin aiki na tsawon wata tara da ƙungiyar malaman jami’o’in ƙasar nan ta yi, da yawan ɗaliban jami’o’i sun nuna rashin shirinsu na komawa makarantar a lokacin da aka sanar. “Ban jima da samun gurbin karatu na digiri na biyu a bangare nazari kan sadarwa ba. Amma sam bana…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Ya Bada Umarnin Biyan Tsoffin Ma’aikata Haƙƙoƙin Fansho

Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta fitar da Naira biliyan 11.82 da nufin a biya tsofaffin ma’aikata hakkokin da su ke bi a karkashin tsarin fansho na CPS. An ruwaito cewa za a biya tsofaffin ma’aikatu da su ka yi aiki a hukumomi da ma’aikatun gwamnatin tarayya shekarun da suka wuce gaba daya ba tare da wani jinkiri ba. Babban jami’in hukumar kula da fansho na kasa ta PenCom, Peter Aghahowa, ya bayyana wannan a ranar Laraba, 6 ga watan Junairu a yayin wata tattaunawa da ya…

Cigaba Da Karantawa

Hatsari Ne Babba Yi Wa ‘Yan Najeriya Rigakafin CORONA – Masana

Masana ilimin Kwayoyin cututtuka a tarayyar Najeriya sun shawarci Gwamnatin Tarayya game da sayen maganin rigakafin COVID-19 a wannan lokacin, suna masu cewa ba shi da bukatar gabatar da shi yanzu ga ‘yan Najeriya, duba da irin hatsarin da ke ɗauke da shi. Wata ƙwararriyar masaniyar kwayar cutar a Cibiyar Nazarin Likitocin Najeriya, Farfesa Rosemary Audu, ta bayyana hakan a wata hira da ta yi da wakilin jaridar The Punch, ta ce ba za a bukaci allurar rigakafin ba idan kashi 70 cikin 100 na al’ummar kasar nan sun samar…

Cigaba Da Karantawa