Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane Da Kona Buhunan Masara A Kasuwar Giwa

‘Yan bindiga da dama sun rasa rayukan su a yayin harin da suka kawo a yankin Galadimawa dake karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna. An kashe ‘yan bindigan ne a yayin da suka kawo farmaki a kasuwar Galadimawa mai ci mako-mako a yammacin yau Laraba, inda ‘yan banga guda biyu da wasu mazauna garin su biyar suka rasa ransu. Majiyarmu ta tabbatar da cewa ‘yan bindigan sun dira kasuwar ne da misalin karfe hudu na yamma inda suka bude wuta kan ‘yan bangan, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar biyu…

Cigaba Da Karantawa

2023: Ka Fito Da ‘Ya’yanka Su Taya Yaƙin Neman Zaɓe – APC Ga Kwankwaso

Jam’iyyar APC a jihar Kano ta mayarwa tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, martani kan jawabin da ya yi kan zaben 2023. Shugaban jam’iyyar na jihar na rikon kwarya, Abdullahi Abbas, ya yi kira ga Kwankwaso cewa ya fito da yaransa na cikinsa lokacin da zai fara yakin neman zabe a 2023. Abbas ya bayyana hakan ne yayin rantsar da kwamitocin gudanarwa na jam’iyyar a kananan hukumomin jihar 44. Martanin ya biyo bayan jawabin da Kwankwaso yayi cewa 2023 sai dai a mutu amma ba zasu yarda da ‘inconclusive’…

Cigaba Da Karantawa

Titunan Abuja: Buhari Ya Amince Da Fitar Da Biliyan 44

Majalisar zartarwar Nijeriya ƙarƙshin jagorancin shugaba Muhamamdu Buhari ta amince da sakin sama da naira bilyan 44 domin bada kwangilar samar da tituna a Abuja. Aikin wanda zai gudana ƙarƙshin ma’aikatar kula da babban birnin da kuma ma’aikatar ayyuka da gidaje ya ƙunshi inganta samar da ruwan sha, da kuma samar da tituna a sassan ƙwaryar birnin. Jaridar The Nations ta ambato ministan watsa labaran Nijeriya Lai Muhammad na cewa an amince da sakin Naira Biliyan 31,630,221,349 a kan waɗannan ayyuka. Shi ma ministan ayyuka da gidaje Babatunda Fashola, ya…

Cigaba Da Karantawa

Za A Yi Ƙazamar Zanga-Zanga Muddin ASUU Ta Cigaba Da Yajin Aiki – Ɗalibai

Kungiyar daliban Najeriya ta yi kira da babbar murya ga ɗaliban Najeriya cewa su shirya afkawa cikin wata ƙazamar Zanga-Zanga muddin Kungiyar malamai masu koyarwa a jami’o’i ASUU suka sake fadawa yajin aikin a Najeriya. Shugaban kungiyar ɗaliban NANS, Sunday Asefon, ya sanar da hakan a wata tattaunawa da manema labarai da yayi a ranar Alhamis ɗin nan a birnin tarayya Abuja. Kwamared Asefon ya ce abun kunya ne da takaici yadda ASUU take sake barazanar shiga sabon yajin aiki bayan ɓata wa daliban Najeriya watanni tara a banza, da…

Cigaba Da Karantawa

Borno: An Bankaɗo Ma’aikatan Bogi Dubu 22,556

Gwamnatin jihar Borno ƙarƙashin jagorancin Gwamnan jihar Farfesa Babagana Umara Zulum ta bankaɗo malaman bogi da ma’aikatan ƙananan hukumomin dake jihar kimanin 22,556 a wani yunkurin tantance ma’aikata da malamai da Gwamnatin jihar ta bayar da umarnin aiwatarwa. Alƙaluman sun nuna kimanin ma’aikatan bogi 14,662 aka gano a ƙananan hukumomin jihar yayin da aka gano wasu malaman karya har 7,794 a ɓangaren ilimi. Da ya ke gabatar da rahoton, shugaban kwamitin tantance malaman firamare, Dr. Shettima Kullima, ya ce, tantancewar ta samarwa jihar rarar kuɗi sama da miliyan 183 da…

Cigaba Da Karantawa

Neja: Fitaccen Malamin Addinin Musulunci Sheikh Lemu Ya Rasu

Sheikh Lemu ya rasu ne da sanyin safiyar yau Alhamis a birnin Minna na jihar Naija ya rasu yana da shekara 91 a duniya. Ɗaya daga cikin ƴaƴan marigayin, Nuruddeen Lemu, wanda ya tabbatar da rasuwar mahaifinsu, ya ce idan anjima kaɗan za a soma shirye-shiryen binne shi. Marigayi Sheikh Lemu ya soma karatunsa na addini da na boko a Najeriya inda daga bisani ya tafi Ingila ya kammala Digirinsa na farko a kan African and Oriental Studies a shekarar 1964 a makarantar da a takaice ake kira SAOS. Ya…

Cigaba Da Karantawa

Kano: Hukumar Tace Fina-Finai Za Ta Bijiro Da Sabbin Matakai A Kannywood

Shugaban Hukumar tace fina-finai da daba’i ta Jahar Kano Malam Ismail Na’abba Afakallahu ya sha alwashin tsaftace fina-finan da ake saki ta YouTube. A yayin ziyararmu ga shugaban hukumar mun tattauna muhimman batutuwa wadanda suka shafi masana’antar shirya fina-finai.Malam Afakallahu mutumin kirki mai karamci da haba-haba yana da sakin jiki da tarairayar Bako yayi matukar godiya bisa ga shawarwarinmu musamman aniyarmu ta ganin an tsaftace fina-finai an kuma inganta su tun daga tushen su. Mun yi nazarin hana fim ba zai zamo mafita ba, domin zamani ya zo da fasaha…

Cigaba Da Karantawa

Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Bindige Tsoho Ɗan Shekara 89 Da Yin Gaba Da Matarshi

A dare ranar Talata ne wasu ‘yan bindiga dauke da manyan bindigogi, suka kai hari a Kauyen Gwammata, da ke cikin karamar hukumar Batagarawa a jihar Katsina, inda suka kashe Mai Unguwar garin, Alhaji Ibrahim Mai Bale, dan shekara tamanin da tara da kashe dansa Da’u Ibrahim Mai Bale har lahira kuma suka sace Matarsa, Hajia Duduwa Ibrahim Mai Bale, yar shekara saba’in da daya. Majiyarmu ta tabbatar mana da cewa da misalin karfe sha daya da rabi na daren jiya, inda gidan Mai Unguwa, aka gwada masu Gidan, ba…

Cigaba Da Karantawa

Gaskiyar Dalilin Da Ya Sa Ganduje Sauke Sunusi Daga Sarauta – Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya maida martani game da wasu kalamai da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi a kan tsige tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II daga Sarautar Kano. Tsohon Gwamnan Kwankwaso ya fitar da jawabin da ya yi wa take da “Ganduje and the blabbering of an imposter” (Wato Ganduje da ƙoƙarin ɓoye gaskiyar tarihi) ta bakin babban sakatarensa, Malam Muhammad Inuwa Ali. Ya bayyana cewar “Hankalin Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ga wani tarin karya da kokarin juya tarihi kuru-kuru da gwamnan Kano…

Cigaba Da Karantawa