A Ceto ‘Yata Kamar Yadda Aka Ceto Ɗaliban Ƙanƙara – Mahaifin Leah Sharibu

Mahaifin Leah Sharibu Mista Nathan Sharibu ya fito fili ya koka dangane da cigaba da rike diyarshi Leah Sharibu tsawon lokaci da kungiyar Boko Haram ta yi, inda ya yi kiran da a gaggauta sakin diyar tashi kamar yadda aka sako ‘yan makarantar Kankara daga hannun ‘yan ta’adda. Leah Sharibu na ‘yar shekara 14 lokacin da yan ta’addan Boko Haram suka saceta ranar 19 ga Febrairu, 2018, tare da kawayenta 110 a makarantarsu, GGSS Dapci dake karamar hukumar Yunusari ta jihar Yobe. Tun daga lokacin ta kasance a hannunsu saboda…

Cigaba Da Karantawa

Katsina: Kotu Ta Bada Umarnin Kama Mahadi Shehu

Alkalin Kotu Shari’ar Musulunci da ke Katsina, wato (Upper Shari’a ii) mai shari’a Sagir Imam ya bada umurnin kamo dan gwagwarmayar nan, Alhaji Mahadi Shehu, dan asalin jihar Katsina azaunin garin Kaduna, bisa karar da sakataren gwamnati jihar Katsina, Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa ya shigar a gabanta, akan zargin bata masa suna. Mai shari’a ya bada umurnin biyo bayan wani hukunci da ya yanke a ranar (16/12/2020) kan yadda aka isar da sakon sammace da aka hannan ta mashi a Abuja, inda lauyan sa ya ce ba abi hanyar da…

Cigaba Da Karantawa

Ina Baƙin Cikin Har Yanzu ‘Yan Najeriya Basu Fahimci Alherin Buhari Ba – Lai Mohammed

Ministan yaɗa labarai da al’adu Alhaji Lai Mohammed ya bayyana nadamarsa guda ɗaya da yake ciki a matsayinsa na minista ƙarƙashin mulkin Buhari. A cewarsa, nadamar tasa bai wuce yadda wasu ƴan Najeriya ke ƙin yabawa gwamnati duk da irin namijin ƙoƙarin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ke yi da ɗan abin da ke a hannunsa. Lai Mohammed, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta musamman da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Abuja. Ya ce duk da ƙarancin kuɗaɗe, babu gwamnatin da ta taɓa kafa tarihin gwamnatin Buhari…

Cigaba Da Karantawa

Gwamnatin Tarayya Ta Bayar Da Hutun Kirsimeti Dana Sabuwar Shekara

A madadin Gwamnatin tarayyar ma’aikatar harkokin cikin gida ta fitar da sanarwar hutun ta bakin Ministan harkokin cikin gidan Mista Rauf Aregbesola. Gwamnatin ta ayyana tarar Jumaa 25, da ranar Litinin 28 na wannan watan na Disembar 2020 a matsayin ranakun hutun Kirsimiti. Har ila yau hutun ya hadar da ranar Jumaa 1, watan Janerun Shekarar 2021, don murnar sabuwar shekarar, inji Rauf. A madadin Ministan, sakataren dindindin na maaikatar harkokin cikin gidan Dakta Shuaib Belgore, ne ya tabbatar da hakan yau laraba, sun yi kira ga mabiya Addinin Kirista…

Cigaba Da Karantawa

Da Ɗumi-Ɗumi: Ƙungiyar Malaman Jami’o’i Sun Janye Yajin Aiki

Labarin da ke shigo mana a yanzu yanzu na nuna cewa kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ta janye daga yajin aikin da ta kwashe watanni tara tana yi. Shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi, ya bayyana hakan ne a hirarsa da manema labarai da safiyar yau Laraba, 23 ga watan Disamba, 2020 a birnin tarayya Abuja. Sanarwar ta biyo bayan ganawar kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya tun daren jiya Talata wadda aka shafe tsawon lokaci ana tattaunawa. Ogunyemi ya kara da cewa mambobin kungiyar ASUU sun janye yajin aikin ne da…

Cigaba Da Karantawa

‘Ya’yana Huɗu CORONA Ta Yi Wa Mummunan Kamu – Boss Mustapha

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustpha, ya ce ‘ya’yansa hudu ne suka kamu da muguwar cutar korona, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito. Mustapha, wanda shine shugaban kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar korona, ya sanar da hakan ne a wani bayani da yayi a Abuja a ranar Litinin. Ya ce daga cikin iyalinsa da cutar ta kama har da yaro mai shekara daya. Sakataren gwamnatin tarayyan ya killace kansa a makon da ya gabata sakamakon mu’amala da yayi da masu cutar. Ya ce a yayin da shi…

Cigaba Da Karantawa

‘Yan Adawa Ne Kaɗai Ke Cewa Ba A Samu Tsaro A Najeriya Ba – Garba Shehu

Kakakin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ya bayyana cewa, ceto daliban Kankara alama ce da ke nuna cewa gwamnatin tarayya a tsaye take wajen ganin ta magance matsalar tsaro. Ya ce hatta wanda ba dangin wadannan yara ba, su yi matukar farin ciki da ceto yaran, kuma ga duk mutane masu tunani me kyau ya kamata su yi farin ciki da hakan. Yace amma akwai wanda ke da matsala masu son saka damuwa a tsakanin al’umma wanda ke shakkun kokarin gwamnatinsu na kawar da matsalar tsaro. Ya bayyana…

Cigaba Da Karantawa

Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Sace Basarake Da Mutane 15

‘Yan bindiga dauke da bindigogi sun kai hari a kauyen Kaigar Malamai da ke karamar hukumar Danmusa, a jihar Katsina, inda suka sace mutane goma sha shida ciki har da Maigarin Kaigar Malamai, Kabir Mai Unguwa. Majiyarmu ta tabbatar mana cewa ‘yan bindigar sun zo ne a tsakar daren shekaran jiya litinin, wayewar safiyar jiya talata, sun kwashe tsawon awowi suna harbe-harbe, sun jiwa wasu raunuka. Sun shiga gida-gida suna bincike bayan sun tsorata mu, sun tafi da Mai unguwar garin, sun tafi matan sure shidda da ‘yan mata da…

Cigaba Da Karantawa

Saura Ƙiris Ta’addanci Ya Zama Tarihi A Najeriya – Ƙungiyar Gwamnoni

Shugaban kungiyar Gwamnonin Nijeriya, kuma Gwamnan Jihar Ekiti, Mista Kayode Fayemi ya ce sakamakon aiki tukuru da jajircewa da kuma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, an kusa shawo kan matsalar rashin tsaron da ta addabi sassan Nijeriya nan gaba kadan. Mista Kayode Fayemi ya bayyana haka, a Katsina lokacin da kungiyar ta kawo ziyarar jaje da nuna goyan baya ga yunkurin gwamna Masari na kawo karshen matsalar yan bindiga da suka addabi jihar Katsina da sace-sacen mutane da kisan wadanda ba su ji, ba su gani ba. Shugaban kungiyar Gwamnonin Nijeriya,…

Cigaba Da Karantawa