Jawabin Shugaban Kasa: Buhari Ya Haramta Dukkanin Wata Zanga-Zanga A Najeriya

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya dakatar da duk wani nau’in zanga-zanga a fadin tarayyar Najeriya, ba tare da wani ɓata lokaci ba. A jawabin da shugaban yayi a daren Alhamis, ya ce ya dakatar da zanga-zanga ne saboda yadda rajin masu zanga-zangar #EndSARS ya canza zani a fadin tarayyar ƙasar nan, inda ‘yan banin na iya masu ɓoyayyiyar manuf suka kwace abin. Shugaban kasan yace: “Saboda haka ina kira ga matasanmu su daina zanga-zanga kuma su shiga tattaunawa da gwamnati wajen neman mafita.” “Ya zama wajibi a gare in muku…

Cigaba Da Karantawa

Na Gagara Magana Da Buhari Har Yanzu – Babajide

Gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu, ya ce har yanzu bai samu yin magana da shugaban kasa Muhammadu Buhari ba, kan hargitsin da aka samu a Lekki Toll Gate, ranar Talata. A wata zantawa da aka yi da shi gidan talabijin na Arise TV a ranar Alhamis, Gwamnan ya ce sau biyu yana kokarin son yin magana da shugaban kasar amma bai yi nasara ba. Ya ce a karo na farko da ya kira ofishin shugaban kasar, an sanar da shi bai shigo ofishin ba, da ya sake kira na biyu…

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Alhamis, biyar ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da biyu ga watan Oktoba, shekarar 2020. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi kiran a yi hakuri tare da fahimtar kokarin da gwamnati ke kan yi don biyan bukatun masu zanga-zanga. Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya yi kira ga shugabannin al’uma su taimaka su sa baki don kwantar da tarzomar da matasa ke kan yi. Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar,, da Obasanjo, da Oni…

Cigaba Da Karantawa

#EndSARS: Na Gargaɗeka Da Kisan Masu Zanga-Zanga – Obasanjo Ga Buhari

Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya yi tir da amfani da karfi da sojoji su ka yi wajen tasa keyar masu zanga-zanga a Legas, lokacin da suke Zanga-Zangar Lumana. Cif Olusegun Obasanjo ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ba ta dauki duk sauran matakan da ya kamata kafin ta kai ga baza sojoji ba. Obasanjo ya yi wannan bayani ne a wani jawabi da ya fitar a game da murkushe masu zanga-zanga da jami’an tsaro ke yi, a cigaba da Zanga-Zangar EndSARS da ta shiga makwanni biyu a na…

Cigaba Da Karantawa

Fitintinu: Sarkin Musulmi Ya Ayyana Juma’a Ta Zama Ranar Addu’a Ta Musanman

Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta shari’ar Musulunci a Najeriya (NSCIA), Alh Muhammad Sa’ad Abubakar, ya alanta ranar Juma’a matsayin ranar addu’a ta musamman ga Najeriya. Sarkin ya umarci Musulman Najeriya su yi addu’a bisa rikicin da yayi sanadiyar asarar rayuka da dukiya a yankin Arewa da Legas, Benin da wasu jihohi. Mai Alfarma ya jaddada cewa addu’a da komawa ga Allah kadai ya rage a yiwa kasar nan domin samun zaman lafiya. Sarkin Musulmi a jawabin da ya saki a Abuja ranar Laraba, ya bukaci dukkan…

Cigaba Da Karantawa

Zamfara: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 22

Yan bindiga sun hallaka akalla mutane 22 a garin Tungar Kwana dake karamar hukumar Talata-Mafara ta jihar Zamfara daren Talata, 20 ga watan Oktoba, 2020, tare da yin awon gaba da wasu mutanen. Wani dan garin mai suna Malam Ahmed Mohammed ya bayyanawa manema labarai cewa ‘yan bindiga sama da 100 sun kai farmaki kauyen misalin karfe 11 na dare kuma suka fara harbe-harbe. “Mutane ashirin da biyu, wanda ya hada da mata da yara aka kashe lokaci guda, yayinda wasu suka gudu cikin daji.” Mohammed ya kara da cewa…

Cigaba Da Karantawa

Shugaban ‘Yan Sanda Ya Bada Umarnin Janye’Yan Sanda Masu Tsaron Manya

Babban Shugaban rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Mohammed Adamu, ya bada umarnin janye dukkan ‘yan sandan da ke tsaron lafiyar manyan mutane a fadin kasar nan, ba tare da wani ɓata lokaci ba. Kamar yadda aka gano, wannan hukuncin ya biyo bayan bukatar sake assasa dokar dakile zanga-zangar EndSARS a tituna, wadda ta ɗauki kimanin makwanni biyu matasa na aiwatarwa. Wannan umarnin na kunshe ne a wani sako da aka mika ga dukkan kwamandojin ‘yan sandan kasar nan a ranar Litinin kuma ya fara aiki nan take. A bisa ga umarnin…

Cigaba Da Karantawa

Ya Kamata Gwamnati Ta Rinƙa Saurarar Koken Matasa – Dattawan Arewa

Ƙungiyar tuntuba ta magabatan Arewa (ACF) a ta yi gargaɗin cewa ya kamata shugabanni a Najeriya su sani cewa, a wani lokaci ne na saurarar buƙatun jama’a, saboda bai dace ba a cigaba da yin biris da matasa da kuma buƙatunsu ba. Dattawan Arewa sun bayyana cewa cigaba da yin ko ina kula da bukatun matasa tare da matsalolinsu kan iya janyo gagarumar matsala a kasa, wadda ba’a san iyakar ƙarshen ta ba. Shugaban Ƙungiyar Dattawan Arewa na ACF, Audu Ogbeh, ne ya bayyana hakan a wani taron tattaunawa na…

Cigaba Da Karantawa