Kano: Rugujewar Gini Ya Hallaka Mutane

Lamarin ya faru ne a jiya bayan mamakon ruwan sama da aka yi. Ginin wanda na kasa ne, ya rufto ne yayin da mutanen gidan suke bacci inda ya danne ‘yan gidan gaba dayansu su 18, inda aka yi nasarar ceton ransu daga makota da kuma jami’an hukumar kashe gobara ta kano. Nan take mutum biyu suka mutu, inda ragowar kuma suka jikkata aka garzaya da su asibiti domin ba su kulawa. Wanan ba shine na farko ba da aka samu rufatawar gini a cikin Kano. Ko a kwanakin bayan…

Cigaba Da Karantawa

Kada Ku Karya Tattalin Arzikin Najeriya Da CORONA – Majalisar Dattawa

Majalisar dattawan Najeriya ta yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a fadin kasar nan da kada su kashe tattalin arzikin Najeriya ta hanyar daukar salon Turawa wurin yaki da annobar korona. Majalisar dattawan ta yi wannan zancen ne a ranar Talata sakamakon sabon salon yaki da cutar korona da aka dauka. Sun samu zantawa tsakanin kwamitin majalisar dattawa da ke kula da sufurin jiragen sama da lafiya, da kuma masu ruwa da tsaki a kan yadda cutar korona ta kasa kamari a Najeriya da sauran kasashen Afrika. Shugaban…

Cigaba Da Karantawa

Kano Ce Kan Gaba Wajen Jin Daɗin Alhazzai A Najeriya – NAHCON

Hukumar Jin dadin Alhazai ta kasa ta bayyana Hukumar Jihar Kano a matsayin hukumar dake kan gaba bisa sauran jihohin kasar, sannan ta kara da cewa hukumar na kula da kuma tabbatar da hanya mafi sauki ga Alhazan jihar. Wannan na kunshe ne cikin jawabin da Babban shuguban Hukumar jin dadin Alhzan ta Kasa Mallam Zikurullah kunle Hassan, bayan ziyar da ya kaiwa mai girma Gwamnan Kano Dr. Abdullahi umar Ganduje a masaukin sa bayan kammala taron Koli a fadar Mulki ta Aso a ranar Litinin din nan. Shugaban Hukumar…

Cigaba Da Karantawa

Bauchi: An Yi Nasarar Damƙe Wanda Ya Yi Wa ‘Yar Sa Fyaɗe

Rundunar Yan’sandan Jihar Bauchi sun damke wanda ake zargin ya aikata fyade ma yar’ cikinsa mai shekaru 15 da haihuwa, da kuma wadansu mutane su sha tara 19 Rundunar yan’sandan ta fitar da wan nan sanarwa ga manema labarai a ranar Talatan nan, ta hannun kakakin rundunar na Bauchi, DSP Ahmed Mohammed Wakil. Kakakin Yan’sandan yace wani mai suna Umar Mohammed dan Shekara wanda ake kira (Wulas) wanda ke zama a Odoji Quarters a garin Azare an kamashi bayan ya yaudare yar’cikinsa mai tabin hankali da naira hamsin 50 kachal,…

Cigaba Da Karantawa

Zaɓen Edo: ‘Yan Takara Sun Ƙulla Yarjejeniya

‘Yan takarar kujerar gwamna daga jam’iyyun siyasa daban-daban a jihar Edo da ke kudancin Nijeriya suka cimma yarjejeniyar zaman lafiya. Kwamitin zaman lafiya na kasa, karkashin tsohon shugaban Nijeriya, Abdussalami Abubakar ne ya shirya zaman yarjejeniyar. Ana dai zaman dar-dar game da zaben gwamnan da za a yi a jihar, ranar asabar mai zuwa, sakamakon rashin jituwar da ake samu tsakanin magoya bayan manyan jam’iyyun siyasar jihar, wato APC da PDP.

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin laraba, ashirin da bakwai ga watan Muharram, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha shida ga watan Satumba na shekarar dubu biyu da ashirin. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 90 a jihohi da alkaluma kamar haka: Legas 33Filato 27Kaduna 17Ogun 6Abuja 4Anambara 1Ekiti 1Nasarawa 1 Jimillar da suka harbu 56,478Jimillar da suka warke 44,430Jimillar da ke jinya 10,960Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,088 Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce ciyo bashi don gudanar da…

Cigaba Da Karantawa

Kaduna: ‘Yan Bindiga Na Neman Miliyan 100 A Hannun Jami’in DSS Da Suka Sace

Rahotanni sun ce ‘yan bindigan sun sace jami’in ne tare da dansa mai shekaru hudu a hanyar Rigachikun zuwa Afaka a ta jihar Kaduna. Jami’in da har yanzu ba a bayyana sunansa ba ya fada hannun masu garkuwar ne a hanyar Rigachikun zuwa Afaka a ranar Litinin kamar yadda majiyarmu ta ruwaito. Rahotanni sun ce ‘yan bindigan sun tuntubi iyalansa sun nemi a biya su kudin fansa Naira miliyan 100 kafin su sako shi. Jami’in da aka yi garkuwa da shi yana aiki ne a matsayin mai kula da inda…

Cigaba Da Karantawa

Zunubi Ne Babba Tura Wa Rarara Kudin Waƙa – Limamin Haɗeja

Sheikh Yusuf Abdulrahman Ya’u, wanda shi ne babban limamin garin Hadejiya, jihar Jigawa, ya yi magana game da kudin da ake tarawa Dauda Kahutu Rarara, inda ya ce a halin da ake ciki, bai kamata a bijirowa talaka da maganar bada gudumuwa domin ayi wa shugaban kasa Buhari wata waka ba. Shehin Malamin ya yi wannan bayani ne a wajen karatun littafin Adabul – Mufrad kamar yadda wani faifen bidiyo da ya shigo hannun mu ya bayyana. Limamin ya ke tsokaci ya na cewa: “Kuma ana wannan yanayin wani ya…

Cigaba Da Karantawa

Duk Wanda Ya Ce Akwai Yunwa A Najeriya Maƙaryaci Ne – Adamu Aliyu

Ɗaya daga cikin manyan na kusa da shugaba Muhammadu Buhari kuma tsohon dan majalisar wakilai, Farouq Adamu Aliyu, ya bayyana cewa duk masu cewa akwai yunwa a Najeriya makaryata ne. Adamu Aliyu ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin hira da yake a shirin gari ya waye (Sunrise) na tashar Channels. Dan siyasan yace a jiharsa ta Jigawa, babu yunwa kuma hakazalika sauran jihohin Najeriya. Yayinda aka yi masa tambaya da rahoton dake nuna cewa Najeriya ce cibiyar yunwa a duniya, Adamu Aliyu yace: “Ban tunanin gaskiya ne saboda jihata…

Cigaba Da Karantawa

Haramta Shiga Amurka Ga Masu Magudi: PDP Ta Jinjinawa Trump

Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ta jinjinawa haramta wa wasu ‘yan Najeriya shiga Amurka da Shugaba Trump yayi a kan aikata magudin zaben da suka tafka a jihohin Kogi da Bayelsa. PDP ta sanar da hakan ne a wata takardar da sakataren jam’iyyar na kasa, Kola Ologbondiyan ya fitar, Kakakin jam’iyyar ya sake bukatar cewa a kara saka takunkumin hana visa a kan iyalan wadanda aka hana Bayan saka wa wasu ‘yan Najeriya takunkumin hana visa sakamakon tafka magudin zaben da suka yi. Babbar jam’iyyar adawar a wata takarda da…

Cigaba Da Karantawa

Haramta Shiga Amurka Ga Masu Magudi: PDP Ta Jinjinawa Trump

Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ta jinjinawa haramta wa wasu ‘yan Najeriya shiga Amurka da Shugaba Trump yayi a kan aikata magudin zaben da suka tafka a jihohin Kogi da Bayelsa. PDP ta sanar da hakan ne a wata takardar da sakataren jam’iyyar na kasa, Kola Ologbondiyan ya fitar, Kakakin jam’iyyar ya sake bukatar cewa a kara saka takunkumin hana visa a kan iyalan wadanda aka hana Bayan saka wa wasu ‘yan Najeriya takunkumin hana visa sakamakon tafka magudin zaben da suka yi. Babbar jam’iyyar adawar a wata takarda da…

Cigaba Da Karantawa