Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mutane 21

Rahotanni sun tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun sace mutum 21 a kauyen Udawa da ke karamar hukumar Chikum, da ke jihar Kaduna. Daga cikin wadanda aka sace akwai ‘yan gida daya mutum 17. Lamarin ya afku ne a wasu tagwayen hare-hare da ‘yan bindigar suka kai a karshen mako, inda 17 daga cikin mutanen da aka sace suka kasance yan gida daya. Malam Hussaini, wani jigo a kauyen Udawa wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce wasu ‘yan bindiga ne suka mamaye yankin sannan suka dinga harbi ba kakkautawa,…

Cigaba Da Karantawa

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Rufe Gidajen Kallon Ƙwallo

Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji na Jihar Kaduna ta rufe wasu manya-manyan gidajen buga cacan kwallon kafa da ke jihar. Hukumar ta ce gwamnatin jihar na bin wadannan gidajen buga cacan kwallon kafa dake kasuwanci a jihar da suka hada da Betnaija, BetKing, Acesss Bet da sauransu. Shugaban sashen gidajen buga wasannin da caca, Liye Anthony ya bayyana cewa akwai akalla gidajen cacan kwallon kafa 1500, kuma za su bisu daya bayan daya su garƙame saboda basu da cikakken rajista da gwamnatin jihar sannan ana bin wasunsu miliyoyin kuɗin haraji da…

Cigaba Da Karantawa

2023: An Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu

Wata kungiyar siyasa mai suna BAT 23, ta kaddamar da yakin neman zabe da kuma tattara masoya ga shugaban jam’iyyar APC, Bola Tinubu a zaben shugabancin kasa da ke zuwa na 2023 a Abuja. An gano cewa Tinubu na kokarin fitowa takarar zaben shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC a kasar nan.Shugaban kungiyar, Umar Inusa, a yayin kaddamar da fara yakin neman zaben a Abuja a ranar sati, ya ce BAT 23 ta hada da dukkan magoya bayan Tinubu daga jihohi 36 na kasar nan tare da birnin tarayya, Abuja.…

Cigaba Da Karantawa

Katsina: Faɗuwar Gini Ya Hallaka Amarya

Da yammacin ranar Juma’ah ne wani munnan lamari ya faru a Unguwar Gafai cikin Birnin Katsina wanda ya saka mutane cikin juyayi da kuka na rasuwar wata baiwar Allah mai suna Fateema Junaidu, ta bar gidan mijinta zuwa Unguwar domin taya wata daga cikin Aminan arziki murnar samun karuwa, ma’ana taje bikin suna. To dayake a Unguwarsu ake sunan wajen gidan mahaifanta, daga gurin sunan taje gidansu domin gaishe da mahaifiyarta, da sauran danginta dake cikin gidan dama yankin Unguwar baki Daya, saboda mafi yawan yan Unguwar ‘Yan’uwan juna ne.…

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin lahadi, ashirin da hudu ga watan Muharram na shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha uku ga watan Satumba, na shekarar dubu biyu da ashirin. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 160 a jihohi da alkaluma kamar haka: Abuja 39Legas 30Kaduna 23Katsina 7Ribas 6Oyo 6Yobe 6Binuwai 3Bayelsa 1Abiya 1Edo 1Ekiti 1 Jimillar da suka harbu 56,177Jimillar da suka warke 44,088Jimillar da ke jinya 11,011Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,078 Sai ranar talata mai zuwa shugabannin…

Cigaba Da Karantawa

CORONA: Mutane 160 Sun Sake Harbuwa A Najeriya – NCDC

Hukumar hana Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 160 a fadin Najeriya. Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:na daren ranar Asabar 11 ga Satumba, shekarar 2020. A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 160 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka: Abuja-39 Plateau-39 Lagos-30 Kaduna-23 Katsina-7 Rivers-6 Oyo-6 Yobe-3 Benue-3…

Cigaba Da Karantawa

‘Yan Bindiga Sun Yi Sansani A Dajin Kano

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya gana da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, a ranar Laraba, 2 ga Satumba, a fadar shugaban kasa kan matsalar tsaro a jihar. Yayin da yake jawabi bayan ganawar, ya ce ya bayyanawa mataimakin shugaban kasa kokarin da sukeyi wajen magannce matsalar tsaro a jihar. Ya ce jami’an Soji tare da sauran hukumomin tsaro na iyakan kokarinsu wajen dakile ‘yan bindigan da suka shiga dajin Falgore. Ya ce jihar na fuskantar kalubale daga dajin Falgore saboda Sojoji na fuskantar matsala wajen dakatar da ‘yan…

Cigaba Da Karantawa

Ku Cire Imani Ku Yi Kisan Gilla Ga ‘Yan Bindiga – Buratai Ga Dakarun Soji

Babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai, a ranar Asabar ya bukaci sojojin Opertion Sahel Sanity su ragargaji ‘yan bindiga da sauran miyagu ba tare da tausayi ko sassauci ba. Ya ce rundunar sojojin ba za ta bawa masu aikata laifuka damar su numfasa ba ko kadan za ta yi musu kisa irin na gilla domin kawo karshen su gaba daya. Buratai ya yi wannan jawabin ne a sansanin sojoji da ke karamar hukumar Faskari na jihar Katsina a yayin da ya kai ziyarar duba yadda aikin…

Mulkin Buhari: Najeriya Ta Kama Hanyar Tarwatsewa- Obasanjo

Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya sake sukar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari inda ya ce ƙasar ta kama hanyar lalacewa kuma kawunnan ‘yan kasar sun rabu sosai ana zaman ‘yan marina. Obasanjo ya yi wannan furucin ne yayin jawabin da ya yi a wurin wani taron da kungiyoyi masu wakiltan yankunan kasar suka hallarta.Taron da aka yi a ranar Alhamis 10 ga watan Satumba a Abuja ya samu hallarci kungiyoyi kamar Afenifere, Middle Belt Forum, Northern Elders Forum, Ohanaeze Ndigbo da sauran su. Tsohon shugaban kasar ya ce bai taba…

Cigaba Da Karantawa

Mulkin Buhari: Najeriya Ta Kama Hanyar Tarwatsewa – Obasanjo