Rashin Ilimin Addini Ne Ke Haifar Da ‘Yan Ta’adda – Sheikh Lau

An bayyana cewar rashin samun ilimin addinin Musulunci yadda ya kamata shine ke haifar da samuwar ‘yan ta’adda musamman a yankin Arewacin Najeriya. Shugaban kungiyar Izala ta ƙasa baki daya Imam Abdullahi Bala Lau ya bayyana hakan lokacin wata ganawa da ya yi da manema labarai a Kaduna. Sheikh Lau ya ƙara da cewar a halin yanzu Ƙungiyar ta su za ta mayar da hankali sosai wajen yin da’awa da karantar da Fulanin Daji da ke rayuwa a rugage, kasancewar yadda ake yawaitar samun ‘yan ta’adda da masu garkuwa da…

Cigaba Da Karantawa

Tsaro: Ganduje Ya Sanya Kyamarorin CCTV A Titunan Kano

Gwamnan jihar kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya kammala aikin sanya kyamarorin sa ido a wasu manyan titunan Kano domin ingantawa da saukaka Ayyukan tsaro A jahar Kano. Salihu Tanko Yakasai, mashawarci na musamman kan harkokin yada labarai ne ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook, inda ya nuna bidiyon jami’an ‘yan sanda da ke kallon motsin mutane da ababen hawa a kan manyan titunan jahar kano Duk da cewa Kano ta kasance daya daga cikin jihohin da suke da zaman lafiya a Najeriya tun shekaru biyar da…

Cigaba Da Karantawa

Babu Inda Ake Shan Fetur Arha A Duniya Kamar Najeriya – Gwamnatin Tarayya

Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, ya bayyana cewa farashin fetur a Najeriya har a yanzu shine mafi karanta a kasashen yammaci da tsakiyar Afrika. Ministan ya bayyana hakan a yayin jawabi ga manema labarai na hadin guiwa wanda ministan wutar lantarki, Saleh Mamman da karamin ministan man fetur, Timipre Sylva suka hada. Mohammed ya ce , duk da halin da tattalin arzikin kasar nan ke ciki, gwamnati ta ci gaba da aiwatar da manyan ayyukanta ballantana biyan albashi. Amma kuma dole ne ta cire wa kanta al’adun da…

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin talata, goma sha tara ga watan Muharram, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da takwas ga watan Satumba na shekarar dubu biyu da ashirin. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 155 a jihohi da alkaluma kamar haka: Legas 42Filato 25Ribas 16Ebonyi 10Abiya 9Abuja 9Ogun 9Katsina 6Kaduna 6Ekiti 4Taraba 4Edo 3Anambara2Akwa Ibom 2Kano 1 Jimillar da suka harbu zuwa yanzun 55,160Jimillar da suka warke 43,231Jimillar da ke jinya 10,868Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,061 Shugaban Kasa Muhammadu…

Cigaba Da Karantawa

Kotu Ta Haramtawa Kantin “Shoprite” Kwashe Kadarorin Sa

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke jihar Lagos, ta ki sauraren uzirin neman janye maganar da ta yi wa katafaren kantin zamani, Shoprite, wanda ta hana ya kwashe kadarorin sa daga Najeriya, saboda ana bin sa bashin dala milyan 10. Shoprite ya garzaya kotu inda ya nemi Mai shari’a ya janye ɗaurin-talalar da ya yi wa kantin na hana shi wasu mu’amaloli da Kadarorin na sa. Mai Shari’a Nicholas Oweibo, ya ce tunda yanzu kotuna duk hutu su ke yi, ba zai iya sauraren bukatar Shoprite ba, sai dai ya…

Cigaba Da Karantawa

Ƙarin Farashin Mai Ya Tabbata Ba Za A Rage Ba – Buhari

Shugaba Buhari ya ce ba a za rage ƙarin kuɗin litar man fetur ba, domin idan gwamnati ta ci gaba da biyan tallafin rarar mai, to tattalin arzikin Najeriya zai shiga garari nan gaba. Mataimakin Shugaban Ƙasa ne ya sanar da wannan bayani, a madadin Shugaba Buhari, yayin da ya wakilce shi a taron kwanaki biyu na Bitar Ayyukan Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya Na Shekara-shekara, a Ɗakin Taro na Fadar Shugaban Kasa. Buhari ya ce annobar cutar Korona ta dankwafar da ƙarsashin da tattalin arzikin ƙasar nan ke da shi, ta…

Cigaba Da Karantawa

Biyayya Ga Kundin Tsarin Mulki Ne Mafita Ga Shugabannin Afirka – Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya roki shugabannin kasashen nahiyar Afrika ta yamma a kan kar su kara wa’adin mulkinsu fiye da abinda kundin tsarin mulkin kasashensu ya ambata. Buhari ya yi wannan kira ne yayin da yake gabatar da jawabin Najeriya a wurin taron ECOWAS na 57 da aka yi a birnin Niamey na kasar Nijar ranar Litinini. Kazalika, Buhari ya shawarci abokansa su mutunta kundin tsarin mulkin kasashensu tare da gudanar da zabukan gaskiya. Hakan na kunshe ne a cikin jawabin shugaba Buhari da kakakinsa, Garba Shehu, ya waallafa…

Cigaba Da Karantawa