Jihar Ribas: Ana Zaman Ɗar-Ɗar Sakamakon Harin Da Aka Kai Wa Hausawa

Mutane biyu ake zargin sun mutu a garin Oyigbo ta jihar Ribas bayan da wasu da ake zargin ‘yan kungiyar IPOB ne su ka kai masu hari. An hallaka wadannan Hausawa ne a inda su ke zama a karamar hukumar Oyigbo kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa a shafin ta na yau litinin 7 ga watan satunba. Wani wanda abin ya faru a gabansa, ya ce miyagun ‘yan kungiyar IPOB sun aukawa wadannan Bayin Allah ne a ranakun Asabar da Lahadi da su ka gabata. Bayan mutum biyu da…

Cigaba Da Karantawa

‘Yan Kasuwa Za Su Fara Cin Gajiyar Dubu 50-50 Duk Wata – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Litinin, ya sanar da cewa, gwamnatin sa ta shirya kaddamar da wata gidauniyar tallafawa matsakaitu da kananan ‘yan kasuwa a Nigeria. A wannan sabon shirin, a cewar shugaba Buhari, gwamnati za ta dinga tallafawa ‘yan kasuwar ne da N50,000 a kowanne wata.Sai dai, gwamnati za ta dauki tsauraran matakai wajen zakulo ‘yan kasuwan da za su ci moriyar wannan tallafi, kuma ‘yan kasuwar za su fito daga kowanne fanni na kasuwanci. Haka zalika, shugaban kasar ya ce a yunkurin gwamnatinsa na farfado da tattalin…

Cigaba Da Karantawa

Rashin Samun Matsaya: Likitoci Sun Tsunduma Yajin Aiki

Likitocin asibitocin kasar za su tafi yajin aiki a sakamakon gaza zama da shugabanninsu da gwamnatin tarayya ta yi a ‘yan kwanakin bayan nan. Bayan tafiya yajin aiki, kungiyar NARD ta yi kira ga sauran kungiyoyin ma’aikatan asibiti su mara mata baya a wannan gwagwarmaya da ta ke yi. Kungiyar NARD ta bukaci unguwan zoma da masu bada magani da sauran likitoci su amsa wannan kira domin ganin an kara yawan alawus din da ake ba su Jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa kungiyar NARD ta na fafatukar ganin…

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin litinin, goma sha takwas ga watan Muharram, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da bakwai ga watan Satumba, shekarar dubu biyu da ashirin. Zuwa asubahin nan akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 100 a jihohi da alkaluma kamar haka: Legas 29Abuja 22Kaduna 19Oyo 7Ebonyi 6Edo 3Katsina 1Ekiti 1Bauci 1Nasarawa 1 Jimillar da suka harbu 55,003Jimillar da suka warke 43,013Jimillar da ke jinya 10,938Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,057 A yau litinin shugaban kasa Muhammadu Buhari zai…

Cigaba Da Karantawa

ECOWAS: Buhari Zai Ziyarci Nijar Yau Litinin

Shugaba Muhammadu Buhari zai ziyarci kasar Nijar a yau Litinin domin halartan taron shugabannin kasan yankin Afrika ta yamma karkashin gammayar ECOWAS. Mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan ranar Lahadi, a shafinsa na Tuwita. Ya ce Buhari zai samu rakiyar manyan ministocinsa kuma zai dawo bayan zaman. Garba Shehu yace: “Shugaba Muhammadu Buhari zai tashi daga Abuja zuwa Niamey, jamhurriyar Nijar domin halartan taron gangamin shugabannin kasar yankin Afrika ta yamma ECOWAS karo na 57. A taron da za’ayi cikin kwana daya, za’a tattauna kan rahoto…

Cigaba Da Karantawa

Ba Mu Fatan Sake Ganin Mulki Irin Na Buhari A Najeriya – Ustas Albani

Malamin ya ce sannanen abu ne idan aka ce matsalar tsaro ta ki ci balle cinyewa a arewacin Nijeriya. Ya kara da cewa da farko mayakan ta’addancin Boko Haram sun addabi yankin Arewa maso gabas, amma yanzu ‘yan bindiga sun gangaro yankin arewa ta yamma da ta tsakiya. Wannan matsalar ta kasance tana ciwa jama’a da dama tuwo a kwarya. Sheik Adam Albani wanda fitaccen Malami ne wanda lamarin ya matukar saka shi cikin damuwa a wani bidyonsa da ya bayyana, inda yake yi wa shugaba Buhari wankin babban bargo.…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Zai Bar Kyakkyawan Tarihi Da Ba Za A Manta Ba – Hadimin Buhari

Tarihin Shugaba Buhari Zai Kasance Mai Kyau Fiye Da Yadda Masu Sukar Sa Ke Shirin Ya Zamoam’iyar APC ta dare kujerar mulki a shekarar 2015 inda ta doke Gwamnati mai ci, ta zo cikin tsammani sosai kan Shugaban Muhammadu Buhari. Shekaru biyar kenan ake ciki, Gwamnatin ta yi aiki ka’in da na’in don ganin ta cika da yawa cikin tsammanin da ake mata, kuma har yanzu tana kai, Ttbbas akwai wasu Hukunce Hukunce masu Sauri da dole ne a dauka don Dai daita kasar akan Tafarki Cigaba mai Dorewa. Don…

Cigaba Da Karantawa

Mata Sun Samu Kyakkyawan Cigaba A Mulkin Buhari – Ministar Mata

An bayyana cewa Mata sun samu kyakkyawan cigaba a ƙarƙashin shugabancin Shugaban kasa Buhari ta fuskoki da dama, kuma hakan wani abu ne na a yaba da nuna godiya akai. Ministar kula da harkokin Mata Madam Pauline Tallen ce ta bayyana hakan, a yayin wata tattaunawa da aka yi da ita a cikin shirin “Baƙonmu Na Mako” da gidan Talabijin da Rediyo na Liberty Abuja ya saba gabatarwa. Ministar ta bayyana cewa Mata a karkashin mulkin Buhari sun samu wakilci, kuma Shugaban ya bada dama sosai domin sauraren koke koken…

Cigaba Da Karantawa