Yaki Da Ta’addanci: Buhari Ya Sayo Jirgin Yaƙi Daga Rasha

Jirgin dakon kaya daga Kasar Rasha ya sauka lafiya a filin jirgin sama na sansanin sojojin saman Nijeriya dake garin Makurdi a jihar Benue. Jirgin ya sauke wani jirgin yaki na zamani mai saukar ungulu kirar Mi-28NE wanda gwamnatin shugaba Buhari ta saya daga Kasar Rasha domin a yaki ‘yan ta’adda. Wannan shine jirgin yaki mai saukar ungulu da Nijeriya ta mallaka wanda babu irin sa a kyau da tsada, gudu da kuma gaggawan kaiwa hari Allah Ya sa su yi amfami da shi yadda ya dace. Daga Datti Assalafiy

Cigaba Da Karantawa

Ciyar Da ‘Yan Makaranta: Mun Kashe Naira Miliyan 500 Lokacin Kulle – Ministar Jin Ƙai

Ministar jin kai da kula da ibtila’i, Sadiya Umar Farouk ta bayyana cewa naira milyan 523.3 gwamnati ta kashe wajen ciyar da yara ‘yan makaranta a gidajen su. Ta bayyana hakan ne a lokacin ganawar manema labarai da kwamitin yaki da cutar Corona virus a jiya Litinin. Ta ce tsarin ba wai na ma’aikatar ta bane kamar yadda wasu ke tunani. Tace kwamitin dake yaki da cutar Corona virus ne ya bada shawarar yin haka aka kuma tattauna har da gwamnoni aka yadda cewa gwamnatin tarayya ta bayar da kudi…

Cigaba Da Karantawa

Ciyar Da ‘Yan Makaranta: Mun Kashe Miliyan 500 Lokacin Kulle – Ministar Jin Ƙai

Ministar jin kai da kula da ibtila’i, Sadiya Umar Farouk ta bayyana cewa naira milyan 523.3 gwamnati ta kashe wajen ciyar da yara ‘yan makaranta a gidajen su. Ta bayyana hakan ne a lokacin ganawar manema labarai da kwamitin yaki da cutar Corona virus a jiya Litinin. Ta ce tsarin ba wai na ma’aikatar ta bane kamar yadda wasu ke tunani. Tace kwamitin dake yaki da cutar Corona virus ne ya bada shawarar yin haka aka kuma tattauna har da gwamnoni aka yadda cewa gwamnatin tarayya ta bayar da kudi…

Cigaba Da Karantawa

Rashawa: EFCC Ta Tsare Kwamishinan Ganduje

Wani rahoton Daily Nigerian ya nuna cewa kwamishanan kananan hukumomi na jihar Kano, Murtala Garo, na amsa tambayoyi a hannun jami’an hukumar hana almundahana da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC. A cewar rahoton, ana binciken kwamishanan ne bisa mallakan wasu manya dukiya a jihar Kano da birnin tarayya Abuja. Kakakin hukumar EFCC, Dele Oyewale ya tabbatar da hakan ga jaridar yayinda aka tambayeshi. Amma ya ce gayyatan kwamishanan kawai aka yi ba garkameshi ba. Ya ce an gayyaceshi ne don bayani kan wasu abubuwa. Majiya ta…

Cigaba Da Karantawa

CORONA: Zamu Sake Rufe Jihar Kaduna – El Rufa’i

Gwamnatin Kaduna ta ce tana duba yiwuwar sake rufe jihar saboda tashin alƙaluman mutanen da cutar korona ke kamawa a baya-bayan nan, “saboda mutane ba sa bin doka”. Yayin zantawa ta musamman da BBC, Gwamna Nasir Elrufa’i ya bayyana fargabar kada ƙaruwar annobar ta fi ƙarfin asibitocin Kaduna bisa la’akari da ganin yadda ƙwayar cutar ke ƙara bazuwa. Alƙaluman da hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ke fitarwa a kullum sun bayyana gano masu cutar korona 54 ranar Juma’ar da ta gabata. “Ranar Juma’a za ka ga mutane sun yi cunkoso,…

Cigaba Da Karantawa

Tsige Sunusi Daga Sarauta Kuskure Ne Babba – Na Abba

Tsohon Kakakin majalisar wakilai daga jihar Kano, Ghali Umar Na’abba ya bayyana cewa cire tsohon satkin Kano, Muhammad Sanusi II daga Sarauta da Gwamnatin jihar ta yi bai kamata ba. Yace idan aka kalli yanayin cire sarkin, hakan na nuna misalin yanda masu mukaman shugabanci ke amfani da karfin siyasa ba ta hanyar data kamata ba. Ghali ya bayyana hakane a hirar da yayi da Sunnews. Yace duka idan ka kalli yanda Majalisar jihar Kano cikin sauri ta amince da kudirin dokar da ya bayar da damar sauke Sarkin, abune…

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin talata, goma sha hudu ga watan Zulhijja, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da hudu ga watan Agusta na shekarar dubu biyu da ashirin. Jiya da safe wuraren karfe bakwai sai ga rahoto ya ishe ni cewa ma’aikatan kwalejojin foliteknik sun soma jin dilin-dilin da ke nuna lissafin watansu na albashi ya daidaita yau hudu ga watan Agusta. Sai dai watan ariyas da suke bi shekara daya da wata hudu ne bai daidaita ba har yau. Yau makarantu…

Cigaba Da Karantawa

Ba A Taɓa Yin Jajirtaccen Shugaba A Najeriya Kamar Buhari Ba – Sanata Ali

Ɗaya daga cikin shakikai, abokin Makarantar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kuma Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC na kasa na riko, Mai wakiltar Arewa Maso Yamma, Sanata Abba Ali ya bayyana cewa yadda ya san halin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na gaskiya da rikon amana, duk wanda ya kama da zanba cikin aminci ko satar dukiyar al’umma ko da dansa ne na cikinsa Ina da yakinin da sai ya hukunta shi muddin aka tabbatar yana da laifi, sai ya hukunta shi. Sanata Abba, ya bayyana hakan ne, a lokacin da yake tattaunawa…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Ya Kashe Najeriya Da Bashi – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC da su ba wa ‘yan Najeriya hakuri saboda nauyin bashin da suka tara wa kasar. Atiku ya ce kamata ya yi gwamnatin Buhari ta amince da laifin jefa kasar nan cikin bashi mai nauyin gaske. Furucin tsohon mataimakin shugaban kasar ya zo ne a yayin da ya ke babatu dangane da koma bayan ci gaba da kasar nan za ta fuskanta sakamakon kantar bashi. Atiku ya ce, “Najeriya na da jimillar bashin ketare na…

Cigaba Da Karantawa

Borno: Sojoji Ne Suka Buɗe Mini Wuta Ba Boko Haram Ba – Zulum

Gwamnan jihar Barno ya bayyana cewa sojojine suka bude masa wuta a Baga, dake karamar hukumar Kukawa ba Boko Haram ba. Gwamnan ya shaida haka a hira da yayi da gidan talbijin din Channels. Ya ce Sojojine suka bude wa tawagarsa wuta a wannan hanya na su saboda basu iya bambamce tawagar Boko Haram ba da na gwamnan. ” Idan sojojin da aka girke a yankin Baga ba za su iya tsare garin ba, ya kamata a canja su a akai su inda za su yi amfani. Zan sanarwa babban…

Cigaba Da Karantawa

Borno: Sojoji Ne Suka Buɗe Mini Wuta Ba Boko Haram Ba – Zulum

Gwamnan jihar Barno ya bayyana cewa sojojine suka bude masa wuta a Baga, dake karamar hukumar Kukawa ba Boko Haram ba. Gwamnan ya shaida haka a hira da yayi da gidan talbijin din Channels. Ya ce Sojojine suka bude wa tawagarsa wuta a wannan hanya na su saboda basu iya bambamce tawagar Boko Haram ba da na gwamnan. ” Idan sojojin da aka girke a yankin Baga ba za su iya tsare garin ba, ya kamata a canja su a akai su inda za su yi amfani. Zan sanarwa babban…

Cigaba Da Karantawa

Badaƙalar NDDC: Akpabio Ya Fallasa Sunayen Wasu Gwamnoni

Rahotanni sun bayyana cewa ministan harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio ya alakanta wasu tsoffin gwamnoni uku da wasu ayyukan kwangiloli da hukumar ci gaban Neja Delta (NDD) ta bayar. A cewar jaridar The Sun, Akpabio ya yi zargin cewa gwamnoni biyu daga jihar Delta sun aiwatar da wasu kwangilolin hukumar. An kuma tattaro cewa ministan ya ambaci sunan tsohon gwamnan Abia a matsayin wanda ya amfana daga kwangilolin. Jaridar ta bayyana cewa sunayen da Akpabio ya ambata a cikin jawabin sun hada da: Emmanuel Uduaghan (tsohon gwamnan jihar Delta) James…

Cigaba Da Karantawa