Shugaba Muhammadu Buhari ya ce jam’iyyarsa ta APC mai mulki ta na da ikon amfani da sojoji wajen karbe jihohin adawa a babban zaben 2019.
A ranar 10 ga watan Agusta, 2020, jaridar The Cable ta rahoto Shugaban kasar ya na cewa duk da damar da su ke da ita, sun zabi su yi adalci a zaben da ya gabata.
Muhammadu Buhari ya yi wannan bayani ne lokacin da ya zauna da gwamnonin yankin Arewa maso gabashin kasara ranar Litinin a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Gwamnonin jihohin hamayya da su ka samu ganawa da shugaban kasar a jiya su ne: Ahmadu Fintiri (Adamawa), Bala Mohammed (Bauchi) da Darius Ishaku (Taraba).
Buhari ya ke cewa: “Gaskiya ne mun rasa wasu jihohi a matsayinmu na jam’iyya da ke kan mulki a kasar da yanzu ta ke tasowa, wanda an saba ganin wannan.
Ina alfahari da cewa ba mu yi rashin adalci ba, wannan ya sa mu ka rasa wasu zabuka duk da mu ne jam’iyya mai mulki. Hakan ya na nufin mu na da kure-kurenmu.
Da sojojin kasa, ‘yan sanda da sauransu, za mu iya doke ku.” inji Shugaban kasar.
A zaben 2019, Ahmadu Umaru Fintri da Sanata Bala Abdulqadir Mohammed sun doke gwamnatocin APC na Jibrila Bindow da Mohammed Abubakar a Adamawa da Bauchi.
Shugaban kasar ya kara da cewa: “Mu na so ne kawai mu nuna maku cewa mu na da tausayi, kuma mu ‘yan Najeriya ne. Za mu cigaba da yin bakin kokarinmu.
A wajen wannan taro shugaban kasar ya ba ‘yan Najeriya hakurin abin da ya faru a baya, ya kuma yi alkawarin gwamnatinsa za ta cigaba da yin bakin gwargwadon abin da za ta iya.
A jawabinsa, shugaban kasar ya koka game da rashin tsaron da ake fama da shi a Najeriya, yayi kira ga jami’an tsaro su dage wajen ganin sun kawo zaman lafiya.