Mininistan wutar lantarki, injiniya Sale Mamman ya nemi gafarar ‘yan Najeriya bisa tsaikon wutar lantarki da aka fuskanta a fa?in ?asar nan a ‘yan kwanakin nan.
A wani sa?o da ya fitar ranar Alhamis, Mamman yace yayi dana sanin irin matsanancin halin da rashin wutar ya haifar wa ‘yan Najeriya. Ministan yace matsalar ta farune daga tashoshin wutar lantarki wa?anda suke da alhakin raba wutar ga ‘yan Najeriya.
“Nayi matu?ar dana sanin ?arancin wutar lantarki a fa?in ?asar nan, da kuma wahalhalun da hakan ya haifar. Ina mai tabbatar ma ‘yan uwana ‘yan Najeriya cewa muna aiki tu?uru wajen ganin komai yadawo yadda yake ko ma yawuce haka.”
“An samu matsalar ne saboda lalacewar da wasu tashoshin wutar lantarkin wa?anda suke aikin raba wutar. Tashoshin da suka samu matsalar sun ha?a da: Sapele, Afam, Olonrunsogo, Omotosho, Ibom, Egbin, Alaoji da kuma Ihovbor.”
Mamman ya tabbatarma ‘yan Najeriya cewa ma’aikatar wutar tana aiki tu?uru don ganin an gyara dukkan matsalolin da ake fuskantar tashoshin samar da wutar lantarki da kuma matsalar man gas da sauransu. Ya kuma ?ara jaddada aniyar ma’aikatar wutar lantarki na dawo da wutar da ake samarwa a farkon wannan shekarar wacce takai 5,600MW.