Ɗaliban Jihohin Mu Zasu Rubuta Jarrabawar WAEC – Gwamnonin Yarbawa

Gamayyar kungiyar Gwamnonin kudu maso yamma jihohin Yarabawa sun cimma matsaya akan bude makarantu a fadin jihohinsu.

Gwamnonin sun cimma matsayar bude makarantun bayan sun gudanar da taro ta Zoom.

Gwamnonin sun ce matakin bude makarantun ya zama dole saboda a baiwa dalibai ‘yan ajin karshe na sakandare damar rubuta jarabawar karshe ta WAEC.

Gwamnonin da suka goyi bayan kudurin sun hada da Gwamnan Legas, Oyo, Osun, Ogun, Ondo da kuma Ekiti.

Matakin da Gwamnonin suka dauka ya saba da na Gwamnatin tarayya inda ta jadada ba za ta bari a yi jarrabawar WAEC ba saboda annobar cutar cobid-19.

Labarai Makamanta

Leave a Reply