?aliban ?an?ara: Karya Shekau Ya She?a Na Cewar Boko Haram Ta Sace Su – Rundunar Soji

Rundunar Sojin Najeriya ta fito fili ta yi bayani dalla-dalla dangane da yadda ta kubutar da daliban sakandiren Kankara ta Jihar Katsina, sa?anin sauran labaran ?anzon kurege da wasu ke ya?awa akai.

Bayan sace daliban a ranar 11 ga watan Disamba, kungiyar Boko Haram ?ar?ashin jagorancin Abubakar Shekau ta dauki alhakin sace daliban, da bugun kirjin cewa sun yi hakan ne domin fa?a?a ?arfin ?ungiyar ta su a sauran yankunan ?asar.

Rundunar sojin Najeriya ta mayar da martanai ga ikirarin shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, akan cewa kungiyarsa ce keda alhakin sace daliban. A cewar rundunar Sojin, ta yi amfani da salo wajen kubutar da yaran don tabbatar da cewa babu wani yaro da aka kashe ko ya ji rauni a hannun ‘yan ta’addar, kuma an yi nasarar ceto su gaba daya.

Mai magana da yawun rundunar soji a kafafen ya?a labarai, Manjo Janar John Enenche, tare da tsohon darekta a bangaren amfani da hikimomin ya?i, Manjo Janar Ahmed Jibrin mai ritaya, sune su ka bayyana hakan.

Manyan sojojin sun fadi hakan ne yayin wani shiri na musamman na gidan talabijin din kasa (NTA) mai taken “Good Morning Nigeria”. Janar Jibrin ya ce, sakamakon sace ?aliban, minista da manyan jami’an tsaron tare da mai bada shawara kan harkar tsaro sun dira a garin ?an?ara.

Ministan tsaro ya bayar da ka’idojin da za’a bi don tabbatar da kowanne yaro ya kubuta ba tare da cutarwa ba, kuma wa?annan hanyoyi aka bi aka ku?utar da yaran salin alin.

Da ya ke mayar da martani a kan ikirarin Abubakar Shekau, shugaban Boko Haram, a kan cewa kungiyarsa keda alhakin sace alhakin daliban, Jana Jibrin ya ce; “Shekau ba shi da damar da zai iya wannan aikin sakamakon kokarin kawar da mayakansa da rundunar Soji ke yi a Arewa maso Gabas.”

A cewar Manjo Jibrin, Shekau mutum ne mai ?i-fa?i da ke son yin amfani da damar sace yaran don kawo hayaniya da rudani.
Kazalika, ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da i?irarin Shekau akan batun garkuwa da daliban sakandiren Kankara.

Wasu ‘yan Najeriya na ganin cewa zai yi matukar wahala ace ba’a rasa rayukan wasu daliban ba da kungiyar Boko Haram ce ta sacesu. Sannan sun kara da cewa rundunar soji za ta fuskanci gagarumar turjiya wajen mayakan Boko Haram da ace sune suka sace daliban makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara.

Related posts

Leave a Comment