Tsohon ?an Majalisar Dattawa mai wakiltar maza?ar Kaduna ta tsakiya majalisar Dattawa Kwamared Shehu Sani, ya ce dole ayi tir da masu ta’addanci da rigar musulunci a kasar Faransa, sai dai wannan bai hana shi yin tir da aikin Shugaba Macron ba.
?an siyasar ya ce babu abin da zai hana a fito a yi tir da abin da shugaban kasar Faransar ya yi na ba masu yi wa addinin musulunci isgilanci goyon-baya.
“Ya kai @EmmanuelMacron, dole ayi tir da duk wani harin ta’addanci ko zagon-kasa da aka yi a kasar Faransa da sunan musulunci, tsantsar hauka ce da tsantsangwaron rashin imani.”
“Mara baya kai-tsaye ko a kaikaice da ka ke yi ga masu bata musulunci ko cin mutuncin Annabi Muhammad (tsira da aminci a gareshi), duk shi ma abin ayi Allah-wadai ne.”
Sani wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya majalisar dattawa tsakanin 2015 zuwa 2019, ya yi wannan magana ne a shafinsa na Twitter a ranar Litinin.