Ɓatanci Ga Annabi: Saudiyya Ta La’anci Faransa

Gwamnatin Saudiyya ta ce “ba zata lamunci kokarin hada addinin Musulunci da ta’addanci ba kuma ta yi Alla-wadai da zanen manzon Allah domin bakantawa wasu rai da Faransa ta yi”.

Saudiyya ta bayyana hakan ne yayinda kasashe Musulmai ke caccakan kasa Faransa bisa goyon bayan zanen isgili ga manzon Allah SAW da shugaban kasan ya amince a rika yi.

Saudiyya ta yi kira ga Faransa da shugabanta su koyi girmama ra’ayoyin mutane da kuma zaman lafiya maimakon amincewa da abubuwan da ka iya tayar da tarzoma da haifar da kiyayya tsakanin al’umma.

Wani ma’aikacin ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya ya bayyana hakan a gidan talabijin na kasar ranar Talata, kamar yadda gidan talabijin na Aljazeera ta ruwaito.

Ya kara da cewa Saudiyya na Allah-wadai da dukkan wani aikin ta’addanci da wani zai yi saboda hakan ba koyarwan addinin Musulunci bane.

Hakazalika, shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya yi kira ga kasashen duniya su kauracewa sayan kayayyakin da ake yi a Faransa yayinda majalisar dokokin kasar Pakistan ta bukaci jakadanta dake Faransa ya dawo gida.

Bugu da kari, kungiyoyin kasuwanci daban-daban na kasashen Larabawa sun alanta yanke alaka ta kasuwanci da Faransa. An yi zanga-zanga a kasashe irinsu Iraqi, Turkiyya, Falasdin, inda aka kona hotunan shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron.

Labarai Makamanta

Leave a Reply