Shugaban Kungiyar Izala a Najeriya Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya yi Allah-wadai da shugaban Faransa Emmanuel Macron, saboda goyon bayan zanen batanci ga Annabi Muhammad.
Da yake jawabi a wani bidiyo da shafin kungiyar na Najeriya ya wallafa a Facebook, shugaban ya ce ba dai-dai bane ƴancin faɗin albarkacin baki ya zama hanyar ɓata addini ko abin da wasu suka yi imani da shi.
”Babu shakka ya kamata shugabanFaransa da sauran ire-irensa su gane cewa addinin musulunci addini ne na zaman lafiya, don haka ko kowanene a duniya ya soki Annabi, dole ne musulmai daga ko ina su kare addininsu”
A cewar malamin Annabi ya zauna da wadanda ba musulmai ba a Madina, amma akwai gurin da basa yarda su taba.
Kalaman Shugaban ƙasar Faransa dai na cigaba da tayar da ƙura a sassa daban-daban na duniya, musanman a yankunan ƙasashen Musulmi, inda tuni wasu ƙasashen suka shelanta ƙauracewa mu’amala da dukkanin wasu kayayyakin da suka fito daga ƙasar ta Faransa.