Ɓatanci Ga Annabi: Ƙungiyar Amnesty Ta Yi Tir Da Hukuncin Kisa

Ƙungiyar Kare Hakkin Bil’adama ta Amnesty International ta yi Allah-wadai da hukuncin kisar da kotun Shari’a ta Kano ta yanke wa mawaƙi, Yahaya Sharif-Aminu saboda batanci ga Manzon Allah (SAW).

Amnesty ta kuma yi kira ga gwamnatin Kano, karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta soke hukuncin, Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis cikin wata sanarwa mai taken, ‘Ya zama dole mahukunta su soke hukuncin kisar da aka yanke wa mawaƙin Kano,’ mai ɗauke da sa hannun kakakinta, Isa Sanusi.

Wani sashi na saƙon ya ce, “Ya zama dole mahukunta a jihar Kano su yi gaggawar soke hukuncin kisa ta hanyar rataya da aka yanke wa Yahaya Sharif-Aminu saboda samunsa furta kalaman batanci da babban kotun Shari’a ta Kano ta yi.”

Kungiyar ta kwatanta hukuncin da rashin yin adalci inda ta kara da cewa ba a yi wa mawaƙin adalci ba yayin shari’ar. “Bugu da ƙari, yanke hukuncin kisa bayan ba ayi adalci yayin Shari’a ba ya keta hakkin ƴan adam na rayuwa. Ya zama dole a saki Yahaya Sharif-Aminu nan take ba tare da wasu ƙa’idoji ba,” inji shugaban Amnesty ta Najeriya, Osai Ojigho.

An kama Sharif Aminu ne tun a watan Maris bayan wasu masu zanga-zanga sun kona gidan iyayensa kuma suka tafi Hedkwatan hukumar Hisbah ta Kano suka nemi a dauki mataki a kansa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply