Ƙungiyar Kasuwanci Ta Duniya: Ngozi Ta Nemi Gudummuwar Buhari

Shugaban kasa, Muhammad Buhari, ya tabbatarwa da Ngozi Okonjo-Iweala, tsohuwar ministar kuɗi, cewa gwamnatin tarayya zata yi duk mai yiwuwa don ganin ta zama shugabar ƙungiyar kasuwanci ta duniya(WTO).

Buhari ya yi alƙawarin ne yayin da Okonjo-Iweala ta kai masa ziyara a fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya, Abuja.

Okonjo-Iweala da Yoo Myung-hee (ministar kasuwanci ta ƙasar koriya ta kudu), sune ƴan takara da suka kai matakin ƙarshe na neman kujerar ƙungiyar kasuwanci ta duniya (WTO).

Duk wadda ta samu nasarar lashe zaben kujerar a tsakaninsu itace za ta kasance mace ta farko da ta taɓa shugabantar ƙungiyar kasuwanci ta duniya tun daga kafa ƙungiyar shekaru ashirin da biyar da suka gabata.

A cewar Buhari,Okonjo-Iweala ita tafi cancanta da samun matsayin idan aka yi duba ga irin ƙwazo da kuma himma da ta ke da shi a gudanar da aikinta a ƙasa dama duniya baki ɗaya.
“Ina mai tabbatar da cewa za muyi duk yadda zamu iya don ganin kin zama shugabar ƙungiyar kasuwanci ta duniya (WTO). “Ba wai kawai don ke ƴar Najeriya ba ce, saboda ke ƴar ƙasa ce mai ƙwazo da kuma aiki tuƙuru.

Kin cancanci hakan.”Acewar Buhari. Buhari ya daɗa tabbatar mata da cewa zai tuntuɓi wasu shugabannin duniya ta hanyar kiran waya da kuma wasiƙa don neman goyon bayansu.

“Na yi irin hakan ga Dr Akinwunmi Adesina da ya nemi Shugaban Bankin cigaban Afirka (AfDB). Dukkaninku kun yiwa kasa aiki a ƙarƙashin jam’yyar PDP. Gabaɗayanku kun cancanta matuƙa,” a cewarsa.

Yayin da ta ke magana a kan goyon bayan shugaban ƙasar, Ngozi ta ce tana alfahirin zama ƴar Najeriya. Ta kuma jinjinawa shugabannin ƙungiyar tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka a bisa nuna kulawarsu.

Ta roƙi Buhari da ya yi yunƙuri na ƙarshe cikin satin nan don ganin Koriya ta sha kaye sannan Najeriya ta samu nasara ta hanyar tuntuɓar manyan shugabannin duniya.

Ta kuma godewa sauran waɗanda suka nuna goyon baya gareta. “Ina matukar alfaharin kasancewa ƴar Najeriya. Na samu goyon baya sosai daga mai girma shugaban ƙasa, shugaban ma,aikata, ministan harkokin ƙasashen waje, ministan masana’antu, kasuwanci da zuba hannun jari.

“Ministocin sun yi aiki tuƙuru don ganin na samu nasara,” a cewar Okonjo-Iweala. “Shugaban ƙasa ya sakani farin ciki, ina alfahari da ƙasata,” a cewarta.

Labarai Makamanta