Ƙungiyar kwatowa talaka hakkokinsu da tabbatar da adalci (SERAP) ta maka Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari a babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja.
SERAP ta maka shugaban kasar ne saboda gaza bayyana sunayen mutanen da gwamnati tace ta kwato biliyan 800 (N800bn) daga wajensu, da kuma ayyukan da aka yi da kudaden.
Shugaban kasar a ranar 12 ga watan Yuni, 2020 ya yi jawabi mai tsayin sakin layi 78, inda ya bayyana cewa gwamnati ta kwato N800bn daga barayin kasa.
Ya sanar da cewa an yi amfani da kudaden da aka kwato wajen gudanar da ayyukan raya kasa a sassa daban daban na kasar.
A takardar karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1064/2020 da aka shigar a ranar Juma’a a kotun, SERAP ta bukaci kotun ta umurci Shugaba Buhari ya wallafa sunayen mutane da aka kwato kudaden daga wajensu.
A cikin takardar, SERAP ta bukaci kotun ta umurci Buhari ya tilasta hukomin yaki da rashawarar su binciki yadda aka rabawa wasu tsiraru N51bn daga asusun gwamnati a shekarar 2019.
Daga cikin wadanda ake karar akwai Abubakar Malami, Antoni Janar na kasa kuma Ministan shari’a, da Zainab Ahmed, Ministar kudi, kasafi da tsare tsaren kasa.