Ya rasu ne ranar Alhamis a wani asibiti da ke birnin Lusaka babban birnin kasar.
A farkon makon nan ne aka kwantar da shi a asibitin saboda yana fama da cutar sanyin hakarkari wato pneumonia a turance. Masu taimaka masa sun ce bai kamu da cutar korona ba.
Mista Kaunda ya kasance daya daga cikin shugabannin Afrika da suka jagoranci kasashensu wajen samun ‘yanci daga turawan mulkin mallaka.
Ya yi mulkin kasar daga in 1964 zuwa 1991.
Wanene shi?
An haifi Kenneth David Kaunda a cikin 1924 kusa da Chinsali da a baya ake kira Arewacin Rhodesia, kuma mutum ne mai addini matuka kamar yadda aka san mahaifinsa.
Yana da zurfin addini kuma shi ma ya zama malami.
Amma ba da daɗewa ba ya bar makaranta ya shiga gwagwarmayar neman ‘yanci daga Turawan Ingila.
Daya daga cikin matakan da ya dauka na farko don nuna adawa da ya mulkin mulukiyya shi ne kaurace wa cin kayayyakin da turawa ke samarwa inda ya koma cin kayan ganye.
Shugaba Kaunda, wanda ko yaushe ke ɗauke da wani farin zanen hannu, ya yi yaƙi da mulkin wariyar launin fata a cikin gida da kuma mulkin tsiraru fararen fata a Zimbabwe.
Amma a cikin gida, ya tilasta bin jam’iyya guda.
A ƙarshe, bayan shekaru 27 a kan mulki, Mista Kaunda ya sauka daga mulki kuma ya sadaukar da sauran kwanakinsa don yaƙi da cutar mai karya garkuwar jiki wato HIV.
Tun a shekarar 1987, ya kasance shugaban Afirka na farko da ya yarda a fili cewa ɗayan yayansa ya mutu sakamakon cutar.