Ƙetare: Shugaban Kasar Chadi Zai Yi Tazarce Karo Na Shida

Jam’iyya mai mulki a Chadi ta amince shugaba Idriss Deby a matsayin ɗan takararta inda zai nemi wa’adi na shida a zaɓen shugaban ƙasar da za a yi a bana.

Deby mai shekara 68 ya shafe shekara 30 kan mulki a Chadi, kuma yanzu ana sa ran zai sake neman ƙarin shekarun a zaɓen watan Afrilu.

Matakin ya haifar da zanga-zanga a ƙasar, inda wakilin BBC a Ndjaména ya ce matasa da mata sun fito saman titi suna zanga-zanga domin adawa da takarar Deby da ke kan mulki tun 1990.

Jami’an tsaro kuma na ci gaba da farautar masu zanga-zanga kuma zuwa yanzu ba za a iya tantance yawan waɗanda aka kama ba ko suka ji rauni.

Duk da daɗewa kan mulki da kuma salon mulkinsa, amma Deby na samun goyon bayan ƙasashen duniya musamman saboda tasirinsa ga yaƙi da ta’addanci a yankin Sahel.

Mafiyawancin Shugabanni a kasashen Afirka ba sa mutunta tsarin yin zango biyu bisa karagar mulki kamar yadda tsarin dimukuraɗiyya ya shar’anta, suka yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima domin dacewa da bukatun su.

Labarai Makamanta

Leave a Reply